Siti Chamamah Soeratno
Siti Chamamah Soeratno | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Yogyakarta (en) , 24 ga Janairu, 1941 (83 shekaru) |
Karatu | |
Makaranta | Universitas Gadjah Mada (en) |
Sana'a | |
Imani | |
Addini | Mabiya Sunnah |
Siti Chamamah Soeratno mace ce malamar Musulunci daga ƙasar Indonesiya kuma tsohuwar shugabar kungiyar Aisyiyah, kungiyar zallan Musulmi mata ta farko a Indonesia. Ita ce kuma tsohuwar shugabar jami'ar Muhammadiya ta Malang kuma kwararriya kan adabin Indonesia. Ta yi aiki a matsayin malama a Jami'ar Leiden, Jami'ar Mercu Buana, Jami'ar Sebelas Maret da kuma Jami'ar Jihar Yogyakarta da sauransu.[1]
Shigar Soeratno kungiyoyin Islama ya fara ne tun farkon rayuwarta. Ta halarci makarantar sakandire ta Muhammadiyya kuma ta zama shugabar kungiyar matasan Aisiyyah a shekarar 1965.[1] Ita ce mai ba da goyon baya ga musuluntar da ilimi, da ra'ayin cewa manufar "Musulunci" ya kamata ya koma fiye da ayyuka na addini kuma ya kamata ya haɗa da duk wani nau'i na rayuwa da kuma magana ga dimokuradiyya, daidaito, adalci da ka'idojin 'yanci kamar " Dabi’un Musulunci."
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 Chamamah Soeratno: Brilliant and Persistent Fighting Against Stagnancy. Copyright © 2016 Universitas Muhammadiyah Malang, 7 December 2014. Accessed 14 December 2016.