So

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
simbol ɗin so (love symbol)
hannuwan wasu masoya da suka riƙe juna
Botoramin soyayya na wiki ( cartoon ɗin so na wiki)
Soyayya
advanced emotion (en) Fassara da theme (en) Fassara
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na experience (en) Fassara, affection (en) Fassara da Emotion
Bangare na theory of emotion (en) Fassara da psychology terminology (en) Fassara
Has characteristic (en) Fassara intimacy (en) Fassara
Hannun riga da Kiyayya

So tabbas kalmar So nada wata So,nada wata daraja da baiwa wadda ta dade tana bawa malaman soyayya wahala bayyana ta ga dalili kuwa,shine:- Sabanin ra'ayoyin da ake samu daga bangarori dabam dabam na mallaman soyayya ko kuma ince masana soyayya a takaice. Hakan yasa ma'anar So tazo da bayanai dabam dabam, inda wannan dalilin yasa masu karatun littafan soyayya suka kasa gane ainihin ma'anar So. Koda yake So yazo da ma'anoni dabam dabam. Amma zamu iya cewa ma'anar so itace tsananin kauna da bukatar kusantar wani mutum. So", wata iska ce mai yawo wanda babu wani dan adam ko dabba da bai shake ta ba. Kusan ince so hantsi ne leka gidan kowa.Kuma So tsurone, hakana yayi daidai da fadar wani marubuci inda yace"So yakan tsuro har yayi saiwoyinsa a cikin zuciyar masoya, saboda haka idan aka tunbudo shi, shi ma sai ya tunbuko zuciyar. Saboda haka sai in ba'ayi sa'a ba sai a rasa Rai. Sannan Kuma bai kyale kowa ba, ba babba ba, ba yaro ba, ba mutum ba, ba aljani, ba dabba ba kai har tsuntsaye na soyayya!. So yana da hadari idan ba'a yi shi da hankali ba. Ga wasu kirarin So: 1. Soyayya ruwan Zuma 2. So gubace 3. So yayi Kama da Madara 4. So mai hana ganin laifi 5. So ginshikin rayuwa 6. So Hakimin zuciya 7. So aljannah duniya da dai sauran su.[1]

Alamomin So kamar haka[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Yawan kallo musamman a sace
  2. Yawan Ambato
  3. Faduwar gaba yayi da aka ambata masoyi, kuwa sunan shi.
  4. Yawan tunanin abunda aka kamu da sonshi.
  5. Tausayin: idan kaga mutum Yana yawan tausayin ka to yana sonka
  6. Kunya: idan kaga kunya ta shiga tsakani masoya biyu to akwai soyayya ta gaskiya

Abubuwa dake gyara soyayya[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Gaskiya
  2. Amana
  3. Kula
  4. Tsafta
  5. Tsari

Abubuwa dake bata soyayya[gyara sashe | gyara masomin]

1. Karya 2. Yaudara 3. Rashin tsafta. 4. Rashin yarda da Kuma zargi dadai sauran su.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Jessica, Murphy (19 February 2020). "An gano maganin ciwon so". bbc hausa. Retrieved 23 July 2021.