Jump to content

Sophie Sow

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Sophie Sow jami'ar diflomasiyyar Burkinabė ce. Ta yi aiki a matsayin Jakadiyar Burkina Faso a Italiya da Asusun Raya Aikin Noma na Duniya (IFAD), [1] Mali da Jamus.

Shugaba Blaise Compaore ya naɗa jakadiya Sow a Italiya a shekara ta 2008. Ta yi zama a hukumance kuma ta gabatar da wasikunta na takaddun shaida ga Shugaban Italiya Giorgio Napolitano a cikin watan Maris 2008.[2]

A cikin watan Janairu 2021 Shugaba Roch Marc Christian Kaboré ya naɗa Sow zuwa Majalisar Tsarin Mulki ta Burkina Faso, tare da wa'adin shekaru tara.[3] Shugaban Majalisar Dokokin Burkina Faso ne ya zaɓe ta a wannan matsayi.[4]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "IFAD provides US$16.2 million to Burkina Faso for Rural Business Development". IFAD. Retrieved 1 February 2021.[permanent dead link]
  2. "Coopération Burkina Faso Italie : L'Ambassadeur Sophie SOW a présenté ses lettres de créance". Lefaso.net. 2 April 2008. Retrieved 1 April 2021.
  3. "Conseil Constitutionnel du Burkina: 3 nouveaux membres installés". burkina24.com. 8 January 2021. Retrieved 1 April 2021.
  4. "Conseil constitutionnel du Burkina : Trois "sages" prêtent serment pour un mandat de neuf ans". Lefaso.net. 8 January 2021. Retrieved 1 April 2021.