Soraya Rahim Sobhrang
Appearance
Soraya Rahim Sobhrang | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Herat, 1958 (65/66 shekaru) |
ƙasa | Afghanistan |
Ƙabila | Hazaras (en) |
Sana'a | |
Sana'a | Mai kare ƴancin ɗan'adam da minista |
Soraya Rahim Sobhrang 'yar siyasar Afganistan, likita, kuma mai fafutukar kare haƙƙin ɗan adam wacce ke aiki a matsayin kwamishiniyar 'yancin mata na Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan Adam mai zaman kanta ta Afghanistan.
An haifi Sobhrang a Herat kuma ta kammala karatun likitanci a Jami'ar Kabul. Daga baya ta yi hijira zuwa Jamus. Sobhrang ta koma Afghanistan a shekarar 1981 don yin aiki a matsayin mataimakiyar ministar fasaha da siyasa a ma'aikatar harkokin mata. [1] A watan Maris na shekara ta 2006, shugaba Hamid Karzai ya naɗa ta a matsayin ministar harkokin mata amma majalisar ba ta amince da takarar ta ba. [2] Ta sami lambar yabo ta shekarar 2010 Front Line Award for Human Rights Defenders at Risk. [3]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Soraya Sobhrang | Gunda-Werner-Institut". Heinrich-Böll-Stiftung (in Turanci). Retrieved 2021-08-29.
- ↑ انوری, رامين (2006). "کابينه جديد افغانستان به پارلمان معرفی شد". BBC Persian (in Farisa). Retrieved 2021-08-29.
- ↑ "Case History: Soraya Rahim Sobhrang". Front Line Defenders (in Turanci). 2015-12-17. Retrieved 2021-08-29.