Souad Bendjaballah

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Souad Bendjaballah
minista

Rayuwa
ƙasa Aljeriya
Karatu
Harsuna Faransanci
Sana'a
Sana'a masana, ɗan siyasa da Mai kare hakkin mata

Souad Bendjaballah lauya ce 'yar kasar Aljeriya, mai fafutukar kare hakkokin mata kuma 'yar siyasa.

Tarihin rayuwa[gyara sashe | gyara masomin]

Souad memba ne na ƙungiyar bincike Tarihin mata a Bahar Rum tare da Fatima-Zohra Guechi kuma ta halarci wannan taron a watan Nuwamba 1999 a Jami'ar Constantine 1.[1] [2] A ranar 8 ga watan Oktoba, 2003, an nada ta Ministar Delegate ga Ministan Ilimi mataki na sama, mai kula da binciken kimiyya . Ta rike wannan matsayi har zuwa shekarar 2012. A ranar 4 ga Satumba, 2012, an naɗa ta Ministar Haɗin kai, Iyali da Matsayin Mata a ƙarƙashin gwamnatin Abdelmalek Sellal. An sake naɗa ta kan mukamin a karkashin gwamnati ta biyu ta Abdelmalek Sellal yayin da aka yi kwaskwarima na Satumba 11, 2013. Ta rike wannan matsayi har zuwa watan Mayun na shekarar 2014.

A shekarar 2017 ta kasance ministar hadin kai.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Fatima Zohra Guechi, « Groupe de recherche « Histoire des femmes en Méditerranée », Insaniyat / إنسانيات, 9, vol. 9, 1999, p. 149-151
  2. Fatima Zohra Guechi, « Femmes du Maghreb », Clio. Femmes, genre, histoire, vol. 9, 1999