Jump to content

Springhill, Nova Scotia

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Springhill, Nova Scotia


Wuri
Map
 45°40′00″N 64°04′00″W / 45.6667°N 64.0667°W / 45.6667; -64.0667
Ƴantacciyar ƙasaKanada
Province of Canada (en) FassaraNova Scotia (en) Fassara
County of Nova Scotia (en) FassaraCumberland County (en) Fassara
Bayanan tarihi
Ƙirƙira 1790
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci
Wasu abun

Yanar gizo town.springhill.ns.ca

Springhill gari ne da ke tsakiyar Gundumar Cumberland, Nova Scotia, Kasar Kanada.

An kafa garin ne a matsayin "Springhill Mines". Ma'adinai na kwal ya haifar da ci gaban tattalin arziki, tare da zamarta a matsayin birni a cikin shekara ta 1889. An kirkiri wurin hao ma'adanai na filin kwal na Springhill a cikin karni na 19, kuma a farkon shekarun 1880 Kamfanin Cumberland Coal & Railway Ltd. da Springhill & Parrsboro Coal & Rail Company Ltd. suke aikin hake-haken ma'adanan. Wadannan kamfanoni sun haɗa kai a 1884 inda suka samar da Kamfanin Cumperland Railway & Coal Company Ltd., wanda masu saka hannun jari suka sayar a 1910 ga kamfanin masana'antu Dominion Coal Company Limited (DOMCO). Dukkanin harkokin hako kwal ya ƙare a yankin a farkon shekarun 1970s. Garin ya shahara ne a dalilin Annobar Ma'adinai na Springhill da kuma kasancewa gida ga tauraruwar wakoki ta duniya Anne Murray, inda aka kafa Cibiyar Anne Murraya garin don girmama ta, kuma ta zamo wajen yawon bude ido.

Ya zuwa shekara ta 2015 dukiyar ma'adinai, tana daga cikin ramuka mafi zurfi a duniya kuma itace ma'adana ta 2 wanda ya kai zurfin ƙafa 14,300, yana cike da ruwa. Sun samar da wurin shakatawa a masana'antar na Springhill tare da wurin dumama jiki. Kayan dumamawa na geothermal daga ruwan ma'adanan da aka yashar yana iya samar da dumama da sanyaya ga manyan gine-gine ta hanyar amfani da famfo mai zafi.[1][2] Saboda ruwa a cikin ma'adinai yana zagayawa ta hanyar convection, rijiyoyi masu zurfi suna samar da ruwan zafin jiki fiye da ruwan cikin kasa mai zurfi iri daya.[3]

A shekara ta 2015 garin Springhill ya zamo a karkashin Birnin Gundumar Cumberland.

Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.


  1. "Large geothermal potential from old coal mine in Nova Scotia | Think GeoEnergy - Geothermal Energy News". www.thinkgeoenergy.com (in Turanci). 9 October 2017. Retrieved 2018-04-19.
  2. "RFP: Minewater Geothermal Study, Springhill, NS, Canada | Think GeoEnergy - Geothermal Energy News". www.thinkgeoenergy.com (in Turanci). 13 October 2016. Retrieved 2018-04-19.
  3. "Geothermal energy from old mines at Springhill, Nova Scotia, Canada" (PDF). Archived from the original (PDF) on 2018-04-20.