Jump to content

Anne Murray

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

 

Murray in 1971
Murray in 1971
Background information
Sunan haihuwa Morna Anne Murray
Born (1945-06-20) Yuni 20, 1945 (shekaru 79)
Springhill, Nova Scotia, Canada
Origin Toronto, Ontario, Canada
Genre (en) Fassara
Singer
Kayan kida Vocals, guitar
Years active 1967–2008
Record label (en) Fassara
Yanar gizo annemurray.com

Morna Anne Murray CC ONS (an haife ta a ranar 20 ga Yuni, 1945) 'yar kasar Kanada ce mai raira waƙa ta pop, waƙoƙin ƙasa, da kuma waƙoƙin zamani, wacce ta sayar da fiye da albam miliyan 55 a fadin duniya a lokacin da ta yi sana'arta na tsawon sama da shekaru 40.[1] Murray ta lashe kyautar Grammys sau hudu ciki har da Kyautar Grammy don Mace ta Musamman a Wasan Murya na wakokin Pop a shekarar 1979.

Murray ita ce mace ta farko ta Kanada da ta taba hawa ta daya a cikin mawakan Amurka kuma ta farko da ta sami rikodi na zinariya don ɗaya daga cikin waƙoƙinta na musamman, "Snowbird" (1970). [2]  Sau da yawa ana ambaton ta a matsayin ɗaya daga cikin mawakan kasar Kanada waɗanda suka yi tasiri a nasarorin 'yan Kanada a sassan duniya kamar su k.d. lang, Céline Dion, da Shania Twain.[3] Murray an san ta da kyautar da ta lashe na Grammy a 1978 (a kasashe da yawa) "Kuna Bukata Na", kuma ita ce mace ta farko kuma 'yar Kanada ta farko da ta lashe kyautar Albam din Shekara a wurin Kyautan Kungiyar Wakoki na Kasa a dalilin albam dinta mai nasarar Gold-plus na 1983 mai suna A Little Good News.

Baya ga Grammys guda huɗu, Murray ta sami lambar yabo ta Juno Awards, lambar yabo ta kiɗa ta Amurka guda uku, da lambar yabo ta Ƙungiyar Kiɗa ta Ƙasa guda uku, da kuma lambar yabo ta Ƙungiyar Kiɗa ta Ƙasar Kanada guda uku. An shigar da ita cikin Zauren Shahararru na Ƙasar Kanada, Zauren Shahararru na Juno, Zauren Shahararru na na Mawallafin Waƙoƙin Kanada, da kuma Zauren Shahararru na Kafar Watsa Shirye-Shirye ta Kasar Kanada. [4] Ita memba ce ta Country Music Hall of Fame Walkway of Stars a Nashville kuma tana da nata tauraron a kan Hollywood Walk of Fame a Los Angeles da kuma cikin Canada's Walk of Fame da Toronto.[5]

A cikin shekara ta 2011, Billboard ta sanya ta a matsayi na 10 a cikin jerin sunayen 50 Masu Fasaha Mafi Girma na har Abada.

An haifi Morna Anne Murray a wani garin hako ma'adanai a Springhill, Nova Scotia, ga iyaye Dr. James Carson Murray, likitan birnin, da kuma Marion Margaret (née Burke) Murray, wata mai aikin jinya na kyauta a garin. Anne tana da 'yan uwa maza guda biyar. Mahaifinta ya rasu daga cutar Leukemia a lokacin yana da shekaru 72 a shekarar 1980. Mahafiyarta ta rasu a ranar 10 Afurelu shekara ta 2006, a shekaru 92, bayan jerin bugun zuciya a lokacin da ake mata aiki a zuciya. Dan karamin kanin ta Bruce ya mutu yana dan shekaru 69 a ranar 15 ga watan Satumban 2020.

Bayan ta nuna sha'awarta sosai a kan waka, tayi karatun fiyano na tsawon shekaru shida. A lokacin da ta kai shekaru 15, Anne tana shiga motar haya duk ranar asabar daga garin Springhill zuwa Tatamagouche, Nova Scotia don koyon waka. Daya daga cikin wasanninta na farko-farko shine wasan ta da wakar "Ave Maria" a yayin bikin kammala karatunta na sakandare a makaranta a shekarar 1962. Bayan kammala karatun sakandare, Anne ta halarci Jami'ar Mount Saint Vincent a Halifax na tsawon shekara daya. Daga baya ta karanci Ilimin Motsa Jiki a Jami'ar New Brunswick a Fredericton. Bayan ta kammala digiri dinta a shekarar 1966, Anne ta karantar da Ilimin Motsa Jiki a Makarantar Sakandare ta Yankin Athena a Summerside, Prince Edward Island, na tsawon shekara daya.

Kanin ta Bruce Murray ya saki wakokin shi da dama,[6] da wakokinsa da dama a cikin Jadawalin RPM a tsakanin 1976 da 1982.[7]

Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.


  1. "Review – Anne Murray takes fans on nostalgic trip". Canada.com. Archived from the original on June 4, 2011. Retrieved February 4, 2010.
  2. "RIAA – Gold & Platinum". RIAA.com. Archived from the original on December 31, 2009. Retrieved February 6, 2010.
  3. "Celebrities: Anne Murray". Archived from the original on February 27, 2012.
  4. "Member of CAB Hall of Fame". CAB Hall of Fame. Archived from the original on March 4, 2016. Retrieved September 1, 2008.
  5. "Songwriters Hall of Fame – 2008 Award and Induction Ceremony". SongwritersHallofFame.org. Archived from the original on May 22, 2009. Retrieved February 6, 2010.
  6. "Discogs entry for Bruce Murray". Discogs.
  7. "RPM Bruce Murray search results". Library and Archives Canada. July 17, 2013.