Celine Dion



Céline Marie Claudette Dion (An haife ta ranar 30 ga watan Maris shekarata 1968) mawaƙiya ce 'yar asalin ƙasar Kanada. An lura da ita domin zazzakan muryarta da kuma fasaha. Dion ita ce a gaba a wajen yawan siyar da wakokin rikodin a Kanada. Kiɗanta sun haɗa da nau'o'i irin su pop, rock, R&B, bishara, da kiɗan gargajiya.
An kuma haife ta a cikin kananan garin Charlman,mai nisankilomita 30 daga Quebec, ta fito a matsayin sarauniya matashi a cikin ƙasarta tare da jerin kundi na harshen Faransanci a cikin shekarar 1980s. Ta fara samun karɓuwa a duniya ta hanyar cin nasara a bikin Yamaha Mashahurin Waƙar Duniya na shekara 1982 da Gasar Waƙar Eurovision na shekarar 1988, inda ta wakilci a kasar Switzerland . Bayan ta koyi Turanci, ne ta shiga cikin Epic Records a kasar Amurka. A cikin shekara dubu daya da dari tara da cesa'in (1990), Dion ta fito da kundi na farko na Turanci, Unison, ta kafa kanta a matsayin ƙwararriyar mawakiyar fafutuka a Arewacin Amurka da sauran yankunan kasashin turanci na duniya. Rikodin nata tun daga lokacin sun kasance cikin turanci da Faransanci duk da cewa ta yi waƙa a cikin Mutanen Espanya, Italiyanci, Jamusanci, Latin, Jafananci, da Sinanci .
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]Rayuwa da Aiki
[gyara sashe | gyara masomin]1968-1989: Rayuwa ta farko da farkon aiki
[gyara sashe | gyara masomin]
An haifi Dion a Charlemagne, Quebec, kilomita 24 (15 arewa maso gabashin Montreal, ƙarama cikin yara 14 awajen mahaifinsu Thérèse (Samfuri:Nee, 1927-2020), mai kula da gida, da Adhémar Dion (1923-2003), Kuma mahauci, duka na zuriyar Faransa.[1] A matsayinta na ƙarama cikin yara 14, Dion ta girma tana sanya tufafi me alamar Ajeni-a-ƙasa kuma tana kwanan akan gado daya tare da 'yan'uwanta mata da yawa.[2] Yayinda take jaririya, ta yi barci a cikin akwati maimakon bargo don yin tattalin kuɗi. Ansha zaluntar ta a makaranta kuma ansha kiran ta "Dodo mai shan jini" saboda girman hakoranta da rashin kaurin fatarta. Har ma 'yan jaridar masu barkwanci na cikin gida sun kira ta "Me hakora irin na kare" a cikin shekarun tasawa na aikinta. Sau da yawa tana magana game da gudu zuwa gida daga makaranta domin takunna kiɗa a cikin gidansu tare da 'yan uwanta maza da mata. "Na kasance koyaushe ina rayuwa kewaye da manya da yara, Mafi yawansu sun girme ni. Na koyi duk abin da nake bukata na sani daga gare su.matukar abu yashafeni, rayuwa ta ainihi ta kasance a kusa da su. " Babbar yayar Dion a lokacin ta kasance tahaura shekaru ashirin, ta yi aure, kuma tana da ciki da ɗanta na farko a lokacin da mahaifiyar Dion, Thérèse, ta kasance da cikin Dion.
Dion ta girma a matsayin mabiyiyar akidar Roman Katolika a cikin talauci, amma ta hanyar labarinta a gida mai farin ciki a Charlemagne . Kiɗa da waka koyaushe ya kasance babban ɓangare na iyalin Dion, kuma an sanya mata suna bayan waƙar "Céline", wanda mawaƙin Faransa Hugues Aufray ya rera shekaru biyu kafin haihuwarta. A ranar 13 ga watan Agustan shekara ta 1973, ta yi waka a bainar jama'a karon farko a bikin auren ɗan'uwanta Michel, tana raira waƙar Christine Charbonneau "Du fil, des aiguilles et du coton".[3] Ta ci gaba da yin wasa tare da 'ya'yan Dan uwanta a cikin ƙaramin mashaya na piano na iyayenta da ake kira Le Vieux Baril, "The Old Barrel".
Ta sha wahalar samun hatsari sau dadama tun tana yarinya, ciki har da wani abin da ya faru a lokacin da take 'yar shekara biyar lokacin da mota ta buge ta yayin da mahaifinta da ɗan'uwanta Clément ke kallo. An kwantar da ita a asibiti na ɗan kan-kanin lokaci tare da rauni. Tun tana ƙarama, take da mafarkin burin na zama mai wasan kwaikwayo. A cikin shekarar 1994 Tayi wata tattaunawa da afili da mutane, ta ambaci "Na rasa iyalina da gidana, amma ban yi nadama da na rasa ƙuruciyata ba. Ina da mafarki ɗaya: Ina so in zama mawaƙiya. " Yayinda take karama Quebec, Dion ta shiga cikin shirye-shiryen (Girl Guide) a matsayin memba na Girl Guides of Canada. [4][5]
A lokacin da take da shekaru 12, tayi hadaka da mahaifiyarta da ɗan'uwanta Jacques don rubuta da kuma rera waƙarta ta farko, "Ce n'était qu'un rêve", wanda fassarar Taken wakar yake a matsayin "Ya kasance Mafarki ne kawai" ko "Babu komai bane face Mafarki". Michel ya aika da nadadden satin muryar zuwaga manajan kiɗa René Angélil, wanda ya gano sunansa a bayan kundin Ginette Reno. [6] Angélil yayi hawaye dajin muryar Dion kuma ya yanke shawarar sanyata ta zama tauraruwa. A shekara ta 1981, ya ba da Jinginar gidansa donmin daukar nauyin nadar sautinta ta na farko "La voix du bon Dieu" wanda daga baya ya zama Mafi shahara na 1 a gida kuma ya sanya ta ta zama taurararuwa a Quebec. Shahararta ta bazu zuwa wasu sassan duniya lokacin da ta fafata a cikin 1982 a gasar Yamaha World Popular Song Festival a Tokyo kuma ta lashe kyautar mawaƙa ta matakin "Top Performer" da kuma lambar zinare don "Best Song" tare da "Tellement j'ai d'amour pour toi".[6]
A shekara ta 1983, bayan da zama yar wasan kwaikwayo yar asalin Kanada na farko da ya sami shedar girmamawa ta zinariya a Faransa don "D'amour ou d'amitié" ("Of Love or of Friendship"), Dion ya kuma lashe lambar yabo ta Félix da yawa, gami da "Mafi kyawun Yan wasa acikin Mata" da "Binciken Shekara". [6] Ƙarin nasara ya zo ne lokacin da ta wakilci Switzerland a cikin Gasar Waƙoƙin Eurovision ta 1988 tare da waƙar "Ne partez pas sans moi" kuma ta lashe gasar ta kusa da Dublin.[7] A lokacin da take da shekaru 18, bayan kallon wasan kwaikwayon Michael Jackson, Dion ta gaya wa Angélil cewa tana so ta zama tauraro kamar Jackson.[8] Ko da yake tana da tabbaci a cikin baiwarta, Angélil ta fahimci cewa ana buƙatar canza yanda ake jama'a suke ganinta don a tallata ta a duk duniya. Ta janye daga filin wasa na tsawon watanni da yawa, a lokacin da tatafi domin ayi mata tiyatar Hakori don inganta bayyanarta, kuma an tura ta zuwa École Berlitz a 1989 don inganta Turanci. A shekara ta 1989, a lokacin kide-kide na yawon shakatawa na Incognito, ta ji rauni a muryarta. Ta tuntubi likitan otorhinolaryngologist William Gould, wanda ya ba ta makurar kulawa domin a yi mata tiyata nan take a kan igiyoyin murya ko kuma kada a yi amfani da su kwata-kwata har makonni uku. Dion ta zaɓi na ƙarshe kuma ya sami horo na murya tare da William Riley.[9][10]
1990-1992: Unison, Dion tana raira waƙa Plamondon, da Celine Dion
[gyara sashe | gyara masomin]Shekaru biyu bayan ta Kamala koyon Turanci, Dion ta fara fitowa a kasuwar Anglophone tare da Unison (1990), wanda aka fara yin rikodin shi tun ta hanyar mawaƙa na Turanci Junior a 1983 kuma daga baya Laura Branigan . [6] Tayi haɗaka da taimakon masu samarwa ciki har da Vito Luprano da David Foster . Kundin ya sami rinjayen tasiri sosai daga kiɗa mai laushi na 1980s kuma da sauri ya sami wani wuri a cikin tsarin rediyo na zamani na manya.
- ↑ "Celine Dion: From the Perche (France) to Las Vegas". perche-quebec.com. Archived from the original on 13 May 2011. Retrieved 23 January 2016.
- ↑ Helligar, Jeremy (1999). "Family Matters". People. Archived from the original on 27 August 2019. Retrieved 17 September 2019.
- ↑ jmaster. "Céline Dion Biography". portrait-star.fr. Archived from the original on 5 April 2012. Retrieved 18 April 2014.
- ↑ Sanz, Cynthia (13 June 1994). "North Star". People. Archived from the original on 21 October 2012. Retrieved 10 February 2012.
- ↑ "Opinion | Celine Dion, Margaret Atwood among long list of Girl Guides". CambridgeTimes.ca (in Turanci). 2 December 2015. Archived from the original on 29 February 2016. Retrieved 23 April 2020.
- ↑ 6.0 6.1 6.2 6.3 "Dion, Celine". Jam!. Canoe.ca. Archived from the original on 29 June 2012. Retrieved 25 September 2013.CS1 maint: unfit url (link)
- ↑ Empty citation (help)
- ↑ "Céline Dion". MTV Artists. Archived from the original on 23 October 2012. Retrieved 27 September 2014.
- ↑ Cite error: Invalid
<ref>tag; no text was provided for refs namedBombardier 2009 172–173 - ↑ Cite error: Invalid
<ref>tag; no text was provided for refs namedGermain p. 279-280