Stephanie Rose ('yar talla)

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Stephanie Rose ('yar talla)
Rayuwa
Sana'a
Sana'a Mai gasan kyau

Stephanie Rose 'yar kasar Philippines - Austiraliya ce, wacce ta rike kambun mace mafi kyawu, 'yar talla, 'yar wasan kwaikwayo kuma mai taimakon jama'a.[1] An ba ta sarautar Miss Philippines-Australia a watan Oktoban 2011, tun daga nan ta ci gaba da yin tallan kayan kawa, wasan kwaikwayo da kuma ayyukan taimako.

Tarihin Rayuwa[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Stephanie Rose a Australiya ga mahaifiya 'yar Philippine wato Chelsea, da mahaifi ɗan Scotland wanda ake kira Timothy. Ita ce babba ga 'yan'uwanta biyu, Liam da Lachlan.

Rose ta fara yin tallan kayan kawa tun tana da shekaru 17, kuma ta samu hutu ne kawai a watan Afrilu 2012 yayin wani tafiya don harkokin jama'a zuwa Manila. Ta fito a shirye-shiryen talabijin da dama akan shirin Eat Bulaga a matsayin alkalin shirin, shirin Showtime! da Kuma shirin Wil Time Big Time. Vic Del Rosario, Shugaban Viva Films Philippines ne ya fara sanya ta a fim, kuma an ba ta kwangilar fim na shekaru 5.[2]

Ta fito tauraruwa a cikin fim din Marvin Ong, Ayoko Na, wanda Carlo Alvarez ya ba da umarni.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Stephanie Rose: Miss Philippines Australia 2011". Philippine Sentinel. 2011-11-06. Retrieved 2013-08-12.
  2. "PASC beauty queens shine in Manila | Ang Kalatas Australia". Kalatas.com.au. 2012-07-15. Retrieved 2013-08-12.