Sunayen gargajiya a kasar hausa

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Sunayen Gargajiya na Al'adar Hausa kamar yadda aka sani Hausa yare ne me cike da al'adu masu ɗibbin yawa.Bayan Sunan Rana,akwai wasu sunaye da ake amfani dasu wajen yin laƙabi da su. A wannan muƙalar,zamu yi bayani ne akan wasu sanannun sunaye da dalilin da yasa ake laƙabi da su.

 1. Ƴanbiyu wannan laƙabi ne da akeyi wa wanda aka haifa su biyu wato tagwaye .
 2. Gambo Shine ko itace wanda aka haifa bayan an haifa ƴanbiyu.
 3. Kadarko Shine wanda aka haifa bayan an haifi Gambo
 4. Talle wanda mahaifiyar sa ta mutu yana jariri.
 5. Audi Shine wanda mahaifin shi ya rasu yana ciki.
 6. Mati ko TankoWadannan sune sunan da ake kiran wanda ya biyo mata a gurin mahaifiya.
 7. Gude ko Delu sune sunayen wanda ake kiran wacce ta biyo maza jerin haihuwa.
 8. Barau Da Barauki Wannan suna,shine ake kiran mutumin da mahaifiyar shi ta hayayyafa amma duk suna mutuwa sai Shi ya rayu.Sannan idan mace ita ce Barauki
 9. Azumi/Ɗan azumi Shine sunan wanda ka haifa a watan Azumi Ramadan.
 10. Goma/Gomandi suna ne da ake kiran wanda aka haifa na goma a jerin haihuwa.
 11. Anaruwa Wannan sunan shine sunan wanda aka haifa a ruwan sama.
 12. Sadau Wannan shine suna da ake kiran wanda aka haifa bayan aure ya mutu tsakanin mata da miji har tayi wani auren sannan ta fito ta aure tsohon mijin ta,sai aka haifi ɗa ,shi ake kira da sadau.
 13. Korau Shine wanda aka saki mahaifiyar shi ta haife shi a gidan mahaifinta.
 14. Shekarau Shine wanda sai da yakai watannin sha biyu,wato shekara a ciki kafin a haifeshi, a madadin wata tara.
 15. Dogara Shine sunan wanda an cire rai da samun haihuwar sa,sannan su a haifeshi.
 16. Bakwaini Shine mutumin da aka haifa bai fi wata bakwai ba.
 17. Cindo Shine sunan da ake kiran wanda aka haifa ta yatsu fiye da biyar ,ko na hannu ko kafa.
 18. Mati : akan kira mutum mati ne idan ya kasan an haifeshi ne bayan an haifi mata ukku kafin a haifeshi
 • Akwai wasu sunaye da dama wadanda ake kiran su da wata sigar ta daban, idan kaji an kira mutum da sunan to ba shine asalin sunan shi bane,misalan da zasu biyo baya zai nuni da asalin sunan da ake nufi.
 1. Garba Duk wanda kaji da wannan suna asalin suna shi Abubakar.
 2. Shagari mai wannan sunan asalin sunan shi Shehu
 3. Shehu duk mai wannan sunan asalin sunan shi Usman

Sunayen da Hausa ta Gada daga Musulunci[gyara sashe | gyara masomin]

Ba anan sunaye a kasar hausa ya tsaya ba akwai wasu sigogi da sunayen da dalilin musulunci ake sa su ,amma ana samun sauya suna zuwa wata siga. misali: Sunan Annabawa asali da gargajiya

 1. Adam - Ado
 2. Yusuf -Isihu
 3. Sulaiman -Sile,Sule
 4. Dauwud - Dauda
 5. Ilyas - Iliya
 6. Yakub -Yakubu

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]