Tahir Bashir Cheema
1 ga Yuni, 2013 - District: NA-168 Bahawalnagar-III (en)
| |||||
| Rayuwa | |||||
| Haihuwa | 11 Mayu 1960 (65 shekaru) | ||||
| Ƴan uwa | |||||
| Ahali |
Chaudhary Tariq Bashir Cheema (en) | ||||
| Sana'a | |||||
| Sana'a | ɗan siyasa | ||||
| Imani | |||||
| Addini | Musulunci | ||||
| Jam'iyar siyasa |
Pakistan Muslim League (N) (en) | ||||
Chaudhry Tahir Bashir Cheema ( Urdu ; an haife shi 11 ga watan Mayu, shekarar 1960) ɗan siyasan Pakistan ne wanda ya kasance memba na Majalisar Dokokin Pakistan, daga Yunin shekarar 2013 zuwa watan Mayu, shekarar 2018.
Rayuwar farko
[gyara sashe | gyara masomin]An haife shi a ranar 11 ga watan Mayun shekara ta 1960. [1] Iyalinsa sun fito daga Yazman, Bahwalpur.
Sana'ar siyasa
[gyara sashe | gyara masomin]Ya tsaya takarar kujerar majalisar dokokin lardin Punjab a matsayin ɗan takarar jam'iyyar Pakistan Democratic Alliance (PDA) daga mazabar PP-231 (Bahawalnagar-VII) a babban zaɓen Pakistan na shekarar 1990 amma bai yi nasara ba. Ya samu ƙuri’u 24,224 inda ya sha kaye a hannun Muhammad Akram ɗan takarar jam’iyyar Islami Jamhoori Ittehad (IJI). [2]
An zaɓe shi zuwa Majalisar Lardi na Punjab a matsayin ɗan takarar jam'iyyar Pakistan Peoples Party (PPP) daga mazabar PP-231 (Bahawalnagar-VII) a babban zaɓen Pakistan na shekarar 1993 . Ya samu kuri'u 36,912 sannan ya doke Muhammad Akram Ɗan takarar jam'iyyar Pakistan Muslim League (PML-N). [2]
Ya tsaya takarar kujerar majalisar dokokin lardin Punjab a matsayin ɗan takarar PPP daga mazaɓar PP-231 (Bahawalnagar-VII) a babban zaɓen Pakistan na shekarar 1997 amma bai yi nasara ba. Ya samu ƙuri'u’u 22,518 inda ya sha kaye a hannun Muhammad Akram ɗan takarar jam’iyyar PML-N. [2]
Ya yi aiki a matsayin Chishtian Tehsil Nazim daga shekarar 2001 zuwa 2004
A cikin shekarar 2004 an zaɓe shi zuwa Majalisar Dokoki ta ƙasa a matsayin ɗan takarar PML-Q a zaɓen bye-zaben a Chishtian
Ya tsaya takarar kujerar Majalisar Dokokin Pakistan a matsayin ɗan takarar Pakistan Muslim League (Q) (PML-Q) daga mazabar NA-190 (Bahawalnagar-III) a babban Zaɓen Pakistan na shekarar 2008 amma bai yi nasara ba. Ya samu ƙuri'u 70,081 sannan ya sha kaye a hannun Abdul Ghafoor Chaudhry . [3]
An zaɓe shi a Majalisar Dokoki ta Ƙasa a matsayin ɗan takarar PML-N, daga Mazabar NA-190 (Bahawalnagar-III) a babban zaɓen Pakistan na shekarar 2013, Ya samu ƙuri'u 83,353 sannan ya doke Ijaz-ul-Haq . [4]
Ya bar PML-N a cikin Afrilun shekarar 2018. A watan Mayun shekarar 2018, ya shiga Pakistan Tehreek-e-Insaf (PTI).
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Detail Information". 21 April 2014. Archived from the original on 21 April 2014. Retrieved 11 July 2017.CS1 maint: BOT: original-url status unknown (link)
- 1 2 3 "Punjab Assembly election results 1988-97" (PDF). ECP. Archived from the original (PDF) on 30 August 2017. Retrieved 12 October 2018. Cite error: Invalid
<ref>tag; name "ecp/pa-88-97" defined multiple times with different content - ↑ "2008 election result" (PDF). ECP. Archived from the original (PDF) on 5 January 2018. Retrieved 12 May 2018.
- ↑ "2013 election result" (PDF). ECP. Archived from the original (PDF) on 1 February 2018. Retrieved 12 April 2018.