Jump to content

Tony Elumelu

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Tony Elumelu
shugaba

Rayuwa
Cikakken suna Anthony Onyemaechi Elumelu
Haihuwa Jos, 22 ga Maris, 1963 (61 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Makarantar Kasuwanci ta Harvard.
Jami'ar Lagos
Jami'ar Harvard
Jami'ar Ambrose Alli
Sana'a
Sana'a Mai tattala arziki, Ma'aikacin banki da philanthropist (en) Fassara
Reception for African Innovators as Part of the U.S.-Africa Leaders Summit

Tony Onyemaechi Elumelu (An haife shine a 22 ga watan Maris a shekarar ta alif dari tara da sittin da uku miladiyya 1963) Shi dai wani masanin tattalin arziki ne, kuma dan-kasuwa, san nan kuma mai son taimakon jama’a ne, mazauni kuma haifaffen dan Afrika . Shine shugaban Heirs Holdings, The United Bank for Africa, Transcorp sannan kuma shine wanda ya kirkiro wata kungiya ta taimakon kananan yan kasuwa a Afrika wacce ake kira da The Tony Elumelu Foundation. Elumelu yanada shedan girmamawa ta The Nigerian National Honours, The Commander of the Order of the Niger (CON) kuma mamba ne a Order of the Fideral Republic (MFR) a shekarar ta 2003. Ya samu shaidan kasancewa mai hazaka a shekarar ta 2019 daga Nigeria’s National Productivity Order.

Elumelu yana cikin mutane dari (100) masu matukar amfani da aka lissafa a cikin mujallar lokuta (Time Magazine) a shekarar ta 2020.

Rayuwa da Ƴan'uwa[gyara sashe | gyara masomin]

An haife shi ne a Jos, Jahar Plateau, Nigeria, a shekarar ta 1963. Ya taso daga Onicha-Ukwu a Karamar Hukumar Aniocha na Jahar Delta. Yana da digiri guda biyu a bangaren tattalin arziki (Economics) daga jami’oin Nigeria, kamar haka: Digirinsa na farko watau (Bachelor Degree) daga Jami’ar Ambrose Ali daku, digirinsa na biyu na kimiyya watau mastas (Maters) daga Jami’ar Lagos. Elumelu ya auri wata malamar likitanci wacce ake kira da Awele Vivien Elumelu a shekarar ta1993, kuma suna da yara bakwai (7) a tare dasu. Yanada 'yan uwa guda hudu (4), daya daga cikinsu shi ne Ndudi Elumelu, wanda ya kasance dan Majalisa ne a Nigeria.

Aiki[gyara sashe | gyara masomin]

UBA CEO Oduoza, AKon, Ayo Shonaiya and Tony Elumelu at UBA House July 2015

Elumelu ya fara aikinsa na farko ne a Union Bank a matsayin dan bautar kasa a shekarar ta 1985. Ya samu kwarewa sosai inda a shekarar ta 2005 ya fara aiki da Standard Trust Bank da kuma United Bank for Africa (UBA) daga baya.

Bayan barin aikinsa daga UBA a shekarar ta 2010, ya samar da kamfani mai suna Heirs Holding wanda ya karkata a bangarori kamar haka: harkoki na kudi, makamashi, dillanci da karimci, harkokin noma, da kuma bangaren kiwon lafiya. Kuma a wannan shekaran ya kirkiro kungiyar The Tony Elumelu Foundation, wanda ta kasance kungiya da take zaune a Afrika kuma kungiyar masu son taimaka ma jama’a na Afrika.

Yayi hidima a matsayin mai bada shawara ga wata kugiya mai suna USAID’s Private Capital for Africa (PCGA). Ya bada gudummawa ga Nigerian President’s Agricultural Transformation Council (ATIC). Ya kasance mataimakin shugaban wata mai suna National Competitiveness Council of Nigeria (NCCN), wanda ya bada gudummawa mai karfi a cikinta, kuma ya zama mai fada aji na kungiyar Aspen Institute Dialogue Series on Global Food Security. Dadin gushi ya gudanar da kungiyar Ministerial Committee domin samar da ingantattun asibitoci da wuraren gwaje-gwaje a duka fadin Nijeriya, a kuma gayyatar da gwamnatin tarayya (Federal Government) da kungiyar samar da aiki na shugaban kasa (Presidential Jobs Board) sukayi masa yayi ikirarin samar da miliyoyin ayyuka a cikin shekara daya. Ya kuma yi hidima a matsayin mamba a kungiyar Global Advisory Board of the United Nations Sustainable Energy for All Initiatives (SE4ALL) da USAID’s Private Capital Group for Africa Partners Forum.

Kungiya[gyara sashe | gyara masomin]

The Tony Elumelu Foundation

Bayan barin aikinsa daga United Bank for Africa a watan July a shekarar ta 2010, sai ya samar da kungiyar The Tony Elumelu Foundation.

Wadansu Gudummuwar daya Bayar[gyara sashe | gyara masomin]

Kasancewarshi a cikin kungiyar Bretton Woods Committee ya kawo hadin kan manyan shuwagabanni cikin harkokin bankunan duniya, wanda wannan ma ya kasance ya kawo cigaban Africa.

Ya kasance shima dan kungiyar Nigerian Leadership Initaitive (NDL) ne.

Ya kasance yanada sa hannu a cikin kafuwar wata kungiya tareda The Tony Blair Africa Governance Initiative (AGI) ta hanyar hadin gwiwa mai karfi da sukayi domin su karfafa bangarorin dogaro da kai ta hanyar janza tattalin arzikin wasu zababbun kasashe a Africa. Wannan hadin gwiwa a kiransa da The Blair_Elumelu Fellowship Programme.

Ya kasance mai-fada aji a kungiyar Africa Energy Leader’s Group (AELG).

Lambobin Yabo da Girmamawa[gyara sashe | gyara masomin]

A shekarar ta 2003, Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta bama Elumelu inkiyar kasancewa dan Order of the Federal Republic (MFR), wanda wannan ya kasance girmamawa ne na kasa baki daya. Kuma a shekarar ta 2006, yaci kyautan wanda ya kasance shugaban yan kasuwan Afirka na wannan shekaran (African Business Leader of the Year) wanda mujallar United Kingdom ta buga a bangaren masu sanya hannun jarin Afirka. A shekarar ta 2009, Shugaban Kasa Umaru Musa Yar’adua ya bukaci da yayi aiki dashi a bangaren kwamitin shugaban kasa na warware matsalolin kudi na kasa (Presidential Committee on the Global Financial Crisis). Haka kuma a shekarar ta 2012, aka bashi lambar yabo na girmamawan kasa akan kasancewa komanda mai bada tsarin Niger (The National Honour of Commander of the Order of the Niger (CON)) saboda gudummuwar daya bada wajen kawo cigaban kasuwancin masu zaman kansu. A wajen bikin shekara-shekara karo na biyar na Economic Forum of the Ivorian National Council of Employers, CGECI Academy, (CGECI) a garin Abidjan a watan Afrilu a shekarar ta 2016 aka bashi lambar yabo na (Lifetime Achievement Award). Kuma dai a wannan shekara ta 2016 aka bashi lambar yabo na kasancewa Dan Nijeriyan da yafi kowa kwazo a wannan shekara (Nigerian Man of the Year) daga jaridar ‘daily times’.

Wallafawa[gyara sashe | gyara masomin]

Ya kasance yayi rubutu akan yayi bincike da kuma daukaka tattalin arzikin Afirka a rubutu daban-daban da yayi a fadin duniya kamar su, Masanin Tattalin Arzikin Kasa (The Economist), Jaridar Bangon Layi (The Wall Street Journal), da kuma Lokutan Harkokin Kudi (The Financial Times).

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]