Jump to content

Turare

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Turare
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na Kwalliya da aroma compound (en) Fassara
Bangare na cosmetic terminology (en) Fassara
Amfani pleasantness (en) Fassara da hiding (en) Fassara
Ƙasa no value
Shafin yanar gizo no value
turaren feshi
wani turaren fesawa
turaren ice na sandal flakes
turaren kwalba

Turare: Turare wasu chakudaddun sinadarai ne masu kamshin dadi. Wadanda ake narke su gami da hade su guri daya tare da ruwa, don su bada cikakken kamshin da ake so, da dai sauran gyare-gyare bayan an gama hada su ana amfani dashi turaren don kamsasa jiki, na mutane ko na dabbobi har da tufafi da masallatu da majami'u don samun gamsasshen kamshi.

turaren tsinke na wuta

Shi Kuma Turare tun fil'azal ana amfani dashi kowane zamani da yadda suke yin nasu ya danganta da yanayin cigaban fasaha da ilimi. Misali yanzu yadda ilimi musamman na tekanolaji ya samu a duniya, ansamu babban ci gaba.

Ire-iren Turare

1. Akwai turare oyel (oil) 2. Akwai na jiki (body spray) 3. Akwai turaren hayaki na iche (insence) 4. Akwai turaren Humra na Amare da dai sauran su.

turaren kwalba kala-kala
kalan wani turare

Turare yanada muhimmanci sosai ga rayuwar dan Adam babu addinin da ya haramta amfani da turare illa dai ma wasu Addinan sun maida shi a matsayin da sunna mai kyau, kamar Addinin Musulunci turare yanada muhimmanci sosai gareshi. [1].

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Matsayin musulunci kan sanya turare a al'aurar mace". BBC Hausa. 23 January 2018. Retrieved 1 July 2021.

.