Usman Sarki

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Usman Sarki
Rayuwa
Haihuwa 1920
Mutuwa 1984
Sana'a

Usman Sarki dan Malam Saidu MP, CFR (An haife shi a shekara ta alib 1920 - Ya rasu a shekara ta alib 1984) shi ne Ministan Cikin Gida na tarayya daga shekara ta alib 1959 zuwa shekara ta alib 1962 bayan ya gaji J. M. Johnson kuma ya yi aiki a matsayin Etsu Nupe na 10 daga shekara ta alib 1962 zuwa shekara ta alib 1969 bayan ya gaji Etsu Nupe Muhammadu Ndayako na 9. Dan uwan sa ne ya gaje shi a matsayin Etsu Nupe Musa Bello na 11.

Tarihi[gyara sashe | gyara masomin]

An haife shi a gidan ma’asaba na masarautar Bida, mahaifinsa Sa'idu Sarki shine Etsu Nupe na 8. Ya fara karatun sa na farko a sanannen makarantar Middle ta Bida daga shekarar 1933 zuwa shekara ta 1943 sannan kuma sai Kwalejin Kaduna a shekarar 1944. A shekarar 1954 ya karanci ilimin cigaban tattalin arziki da kuma karin ilimin halin kirki a Jami'ar Ibadan.

Aiki[gyara sashe | gyara masomin]

Ya fara aikinsa a matsayin injiniya da kuma mai kulawa a karamar hukumar Bida kafin ya zama wakilin tarayya a shekarar 1955 a karkashin kungiyar NPC kuma shi ne sakataren ayyuka da binciken da ya kasance wakilin Tarayya. A shekarar 1960 ya kasance ministan harkokin cikin gida na tarayya kafin ya bar shekarar 1962 ya gaji kawunsa, HRH Etsu Nupe Muhammadu Ndayako wanda ya mutu. SHUGABA Alhaji Shehu Shagari ne ya gaje shi.

Yana daga cikin wakilan Arewa na shekarar 1966 don tattaunawa a tsakanin manyan yankuna bayan juyin mulkin na shekarar 1966.

Mutuwa[gyara sashe | gyara masomin]

Usman Sarki Ya mutune a shekarar 1984 a Sakkwato a ziyarar da ya kai wa mai alfarma Sarkin Musulmi Sir Abubakar III abokin karatunsa kuma an yi masa jana'iza a garin 'Yan Asalin Bida.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

https://books.google.com/books?id=juZyAAAAMAAJ&q=etsu+usman+sarki https://nigerianwiki.com/Usman_Sarki Archived 2022-01-19 at the Wayback Machine https://thenationonlineng.net/ten-years-of-the-13th-etsu-nupe/