Jump to content

Asaba (Najeriya)

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Asaba


Wuri
Map
 6°11′00″N 6°45′00″E / 6.1833°N 6.75°E / 6.1833; 6.75
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
JihaDelta
Babban birnin
Yawan mutane
Faɗi 149,603
• Yawan mutane 558.22 mazaunan/km²
Labarin ƙasa
Yawan fili 268 km²
Altitude (en) Fassara 180 ft
Bayanan tarihi
Ƙirƙira 1884
Bayanan Tuntuɓa
Lambar aika saƙo 320241
Kasancewa a yanki na lokaci
Tsarin lamba ta kiran tarho 056
Wasu abun

Yanar gizo asaba.com
Wurin Asaba a cikin Najeriya
Asaba.
Asaba roundabout delta state

Asaba[1] Birni ce, a cikin jihar Delta, a cikin Najeriya. Tana nan daga yammacin gabar rafin Niger, ta karamar hukumar Oshimili South.[2][3][4] Asaba na da yawan jama'a kimanin mutum 149,603 a kiadayar shekara ta 2006,[5] da yawan mutane a birnin kimanin mutum dubu dari biyar.[6]

An san birnin Asaba da mu'ala iri-iri musamman a dalilin wuraren shakatawa da otel-otel dake garin, gidajen rawa, swuraren kallo na sinima, da wuraren shahulgula iri-iri. Akwai biki da ake gabatarwa duk shekara a garin wanda ake kira Delta Yaddah, ana tara mawaka a taron bikin. Ta'addanci yayi yawa a birnin saboda yawan jama'arta. Ta'addanci sun hada da yankan aljihu, kwace da sauransu. Akwai tsadar rayuwa a garin saboda mutane daga kasashen waje dake shigowa birnin. Gadar Onitsha itace iyaka tsakanin jihar Delta da Anambra, gadar ita ta raba Asaba da Onitsha.

Asalin Kalma[gyara sashe | gyara masomin]

Kalmar Asaba ta samo asali ne daga kalmar Ahabam ma'ana "Na zaba da kyau" ko kuma "I have chosen well" da turanci, kalmar da aka hakayo daga Nnebisi, wanda shine asalin wanda ya samar da Asaba.[7][8][2] Mafi akasarin mutanen Asaba inyamurai ne.

Tarihi[gyara sashe | gyara masomin]

Birnin Asaba ta kasance a da babban birnin yankunan mulkin Turawa na kudanci Najeriya wato Southern Nigeria Protectorate.[9] An samar da birnin a shekara ta 1884.[10] A tsakanin 1886 da 1900, ita ke dauke da kamfanin Royal Niger Company, wanda turawa suka kafa don habaka kasuwanci da fitar da kaya zuwa kasashen turai. Wannan kamfanin a yau shi ake kira da UAC Nigeria PLC. Matafiyin neman ilimi dan Faransa William B. Balkie, lokacin da yake waken yarjejeniyar kasuwanci da shugaban inyamurai Ezebogo a Asaba a ranar August 30, 1885, "Bayan gaisuwar mu, ina magana akan abota, ta kasuwanci, da ilimi, da kuma mafi muhimmanci akan sharrin yaki, da amfanin zaman lafiya, wanda duka anyi maraba da su".[11]

Dangane da fitaccen tarihin Asaba da kuma labarin kasar ta, da kuma tasirinta a Najeriya ta fuskar siyasa da kuma kasuwanci, Ana yi wa Asaba lakabi da cibiyar yankin Anioma.[12]

Labarin Kasa[gyara sashe | gyara masomin]

Asaba na kan wani bisa kwarin rafin Niger, daura da Rafin Anambara. A bayan wadannan rafuka akwai kurgunmin daji mai tarin itace. A tarihance wannan rafin Niger River ya kasance cibiyar sufuri tsakanin kasashen Afurka har zuwa tekun Atlantic Ocean. Asaba ta hada mahada tsakanin yammaci, gabaci da arewacin Najeriya hanyar rafin River Niger daga arewa da kuma gadar Rafin Niger, wanda yake gabas-maso-yammacin yankin kuma babban tambari ne na Najeriya.[2]

Asaba na nan daga degree6 daga arewacin equator, sannan tana da nisan iri daya daga meridian sannan tana da nisan kusan kilomita 160km (mil 100) daga arecin inda ruwan rafin Niger ke gangarawa cikin tekun Atlantic Ocean.[8] Asaba ta mamaye fili mai fadin 300kmsq. Tana da zafi na kimanin 32c a lokaci na rani, sannan da matsakaicin adadin ruwan sama na kimanin millimitoci 2,700m (106 in) a lokacin damuna.

Babban birnin Asaba ya hada sauran makwabtan garuruwa kamar as Igbuzo, Okpanam, Oko, Okwe and Ugbolu wanda ke yankin yammacin River Niger.

Ala'adu[gyara sashe | gyara masomin]

Al'adun Asaba sun ta'allaka kwarau da gaske da soyayyar su ga "Asagba of Asaba", wanda shuwagabanninsu (da ake kira da "Diokpa”) na duka kauyukan garin guda biyar ke kai wa kukansu game da abun da ya shafi mutanen garin.[3] Iyasele na Asaba [Iyase] ke taimakawa wa Asagba wanda shine matsayin prime minista na gargaijya kuma shugaban dattijai [Kamar [Olinzele, Otu Ihaza, Oloto, da dai sauransu.]

Jama'a[gyara sashe | gyara masomin]

Inyamuarai suka kwashe kaso 63% na mutanen garin, kuma mafi akasarin su haifaffun birnin Asaba ne. Asaba ta habaka ta fannin yawan mutane da kusan rabin miliyan (500,000) tun daga lokacin da ta zamo babban birnin Delta. A yanzu ta tara mutane iri-iri wanda ba 'yan asalin birnin bane.[2] Wasu daga cikin yarukan da ke zama a birnin sun hada da Urhobo, Isoko, Ijaw, Hausa, Itsekiri da kuma Yabawa.

Tattalin arziki[gyara sashe | gyara masomin]

Asaba cibiyar gudanarwa ce kuma mazaunin gwamnati wanda aka samar da ita a lokacin kamfanin Royal Niger Company a yanzu (UACN), kuma itace babban birnin gudanarwa na jihar Delta. A dalilin hakan mafi akasarin mutanen birnin ma'aikatan gwamnati ne. Gwamnatin Najeriya a karkashin mulkin gwamnatin Samuel Ogbemudia suka samar da kamfanin Asaba Textile Mills[13] da kuma kamfanin wutar Lantarki na Asaba. A birnin Asaba akwai kamfanoni dake sarrafa magunguna sannan akwai kamfanin sarrafa karafuna. Akwai masu zuwa yawan bude idanu da yawa cikin garin, wannan ya jawo habakar kasuwancin wuraren shakatawa da otel-otel.

Kasuwanni[gyara sashe | gyara masomin]

Akwai manya-manyan kasuwanni guda uka a Asaba wanda suka hada da: kasuwar Ogbe-Ogonogo, kasuwar Cable Point, da kuma kasuwar Infant Jesus.

Wasanni[gyara sashe | gyara masomin]

Filin wasan kwallon kafa na Stephen Keshi Stadium na Asaba, wacce ke da budadden gaba saboda masu kallo daga gari ya dauki nauyin wasanni kwallon kafa da dama tun lokacin da aka gyara ta a karkashin mulkin Senator Dr. Ifeanyi Arthur Okowa, tare da amincewar tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo.[14] Filin shine matsayin filin wasanni na gida na kungiyar kwallon kafa na Delta Force FC.

Sufuri[gyara sashe | gyara masomin]

Jirgin sama[gyara sashe | gyara masomin]

Za'a iya ziyarta birnin Asaba da sauran biranen kewaye ta hanyar filin jirgin sama na Asaba international Airport.

Titin Mota[gyara sashe | gyara masomin]

Babban titin Asaba zuwa Benin titi ne mai matukar muhimmanci saboda shi ya hada garuruwan yammaci da gabacin Najeriya. Sanna har wa yau akwai titin da ya hada Asaba da Ughelli, sannan titin Asaba-Ebu ya hada Asaba da arewacin Najeriya.

Ruwa[gyara sashe | gyara masomin]

Ana iya zirga-zirga ta ruwa a birnin Asaba ta rafin River Niger, wacce ta zagaye yawancin garuruwan Afurka.

Sanannun Mutane[gyara sashe | gyara masomin]

Hotuna[gyara sashe | gyara masomin]

Kara dubawa[gyara sashe | gyara masomin]


Hanyoyin hadin waje[gyara sashe | gyara masomin]

Samfuri:Igbo topics Samfuri:Cities in Nigeria


Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

 1. Isichei, Elizabeth Allo (1997). A History of African Societies to 1870. Cambridge University Press. p. 249. ISBN 0-521-45599-5. Retrieved December 13,2008.
 2. 2.0 2.1 2.2 2.3 "About Asaba". asaba.com/about/. Retrieved April 21, 2016.
 3. 3.0 3.1 "Asaba Progressive Union". www.asabaatl.org/about.html. Archived from the original on May 7, 2016. Retrieved April 22, 2016.
 4. Okenwa Nwosu (Igbo Focus) (January 2, 2014). "The Politics of Second Niger Bridge". www.igbofocus.co.uk. Archived from the original on December 6, 2015. Retrieved April 21, 2016.
 5. "FEDERAL REPUBLIC OF NIGERIA : 2006 Population Census" (PDF). Wayback Machine. Archived from the original (PDF) on March 5, 2012. Retrieved July 25, 2016.
 6. "A History and Tradition". Asaba Online. Asaba Progressive Front. Archived from the original on 2007-09-15. Retrieved June 19, 2007.
 7. "Great Goddess And Shrine Of Asaba People". Leadership. 23 September 2016. Archived from the original on 24 September 2016. Retrieved 4 February 2017.
 8. 8.0 8.1 "Asaba Progressive Union". www.asabaatl.org/about.html. Archived from the original on May 7, 2016. Retrieved April 22, 2016.
 9. "Asaba". www.britannica.com. Retrieved April 24,2016.
 10. Letters from Nigeria,D.W. Carnegie,BiblioBazaar, LLC, ISBN 978-1-103-27100-9
 11. "BAIKIE, WILLIAM BALEOUR (1856). "Narrative of an Exploring Voyage up the rivers of Kwora and Binue commonly known as Niger and TSADDA in 1885 with a map and appendices". ia600303.us.archive.org. John Mueray, Albemarle Street (Published with a sanction of Her Majesty's Government). Retrieved April 24, 2016.
 12. "Anioma: Nigeria 37th State in the Making". umuanioma.com. Retrieved April 22, 2016.
 13. "Samuel Osaigbovo Ogbemudia (1932=2017)". Guardian (Nigeria). 24 March 2017. Retrieved February 18, 2018.
 14. "Delta Obasanjo commissions stephen keshi stadium". Vanguard (Nigeria). November 19, 2018. Retrieved March 31, 2019.
 15. 15.0 15.1 15.2 "Asaba. A long history and Tradition". Asaba Online. 23 August 2009. Retrieved October 11, 2016.
 16. BellaNaija.com (2015-03-02). "Lynxxx: Everybody We Went to Seeking a Record Deal Rejected Us and Then We Decided to Start Our Own". BellaNaija (in Turanci). Retrieved 2021-06-27.
 17. Davis, Todd (2017-02-03). "[INTERVIEW] Afro Pop Sister Trio, SHiiKANE Epitomize Black Girl Magic". Parle Magazine — The Online Voice of Urban Entertainment (in Turanci). Retrieved 2021-06-27.
 18. "Checkout Details Of Emma Nyra's Career, Personal Life And Scandals". Within Nigeria (in Turanci). 2019-04-24. Retrieved 2021-06-27.