Jump to content

Valentin Glushko

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

 

Valentin Glushko
An haife shi 2 Satumba 1908  (1908-09-02
Ya mutu 10 Janairu 1989  (1989-01-11 (shekaru 80)  
Wurin hutawa Kabari na Novodevichy, Moscow
Ilimi Jami'ar Jihar Leningrad
Aiki Injiniya
Ayyukan injiniya
Hanyar horo Injiniya (Kwamfuta)
Cibiyoyin Shirin sararin samaniya na Soviet
Muhimmin zane Almaz
Sa hannu

Valentin Petrovich Glushko (An haife shi 2 ga Satumba 1908 - 10 ga Janairu 1989) ya kasance injiniyan Soviet ne wanda ya kasance manajan Shirin sararin samaniya na Soviet daga 1974 har zuwa 1989.

Glushko ya yi aiki a matsayin babban mai tsara injunan roket a karkashin shirin Soviet a lokacin Gasar sararin samaniya tsakanin Amurka da Tarayyar Soviet, kuma ya kasance mai ba da shawara ga cybernetics a fannin shirin sararin samaniya.

Tarihin rayuwa

[gyara sashe | gyara masomin]

A lokacin da yake da shekaru goma sha huɗu ya kasance mai sha'awar Jirgin sama bayan ya karanta litattafan Jules Verne. An san shi da rubuta wasika ga Konstantin Tsiolkovsky a 1923. Ya yi karatu a makarantar kasuwanci ta Odessa, inda ya koyi aikin ma'aikacin ƙarfe. Bayan kammala karatunsa ya yi aiki a wani masana'antar gyaran ruwa. An fara horar da shi a matsayin mai gyarawa, sannan ya koma mai aiki.