Valerie Ebe

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Valerie Ebe
Rayuwa
Haihuwa 26 ga Maris, 1947 (76 shekaru)
Karatu
Makaranta Jami'ar Najeriya, Nsukka
University of Uyo (en) Fassara
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party

Valerie Maurice Ebe (An haifeta ranar 26 ga watan Maris, 1947). Lauya ce kuma ‘yar siyasa a Nijeriya wacce ita ce mace ta farko da ta zama Mataimakiyar Gwamnan Jihar Akwa Ibom.[1] itace ta farkon mace a jihar akwa ibom wanda sukai takara suka samu.

Rayuwar farko da ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

An haife Ebe a ranar 26 Maris 1947 ga Edidem Paul Bassey, mai mulkin lardin Etoi Clan. Ta yi makarantar firamare ta Holy Child, Calabar sannan aka shigar da ita makarantar Holy Child Secondary, Calabar a 1957 don karatun sakandaren ta. Daga baya ta samu horo ta zama malama a Kwalejin Horar da Malama Mai Tsarki, Ifuho. Ta karanci Tarihi da Archaeology a jami’ar Najeriya, Nsukka sannan daga baya tayi karatun Lauya a jami’ar Uyo . An shigar da ita a matsayin Barista kuma Lauyan Kotun Koli ta Nijeriya a 1998.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]