Volodymyr Borodiansky

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

  

Volodymyr Borodiansky
Minister of Culture and Information Policy of Ukraine (en) Fassara

29 ga Augusta, 2019 - 4 ga Maris, 2020
Yevhen Nyshchuk (en) Fassara, Ihor Zhdanov (en) Fassara - Svitlana Fomenko (en) Fassara
Rayuwa
Haihuwa Novyi Rozdil (en) Fassara, 15 ga Janairu, 1974 (50 shekaru)
ƙasa Ukraniya
Karatu
Makaranta Kyiv National Economic University named after Vadym Hetman (en) Fassara
Sana'a
Sana'a media proprietor (en) Fassara da ɗan siyasa
Kyaututtuka
IMDb nm9596773

Volodymyr Volodymyrovych Borodianskyi ( dan Ukraine  ; an haife shi a ranar 15 Janairu 1974,[1] Novyi Rozdil, Lviv Oblast, Ukraine ) manajan gidan talabijin ne na Ukraine, shahararre ne acikin jama'a, ɗan kasuwa kuma ɗan siyasa.[2] shine Ministan Al'adu, Matasa da Wasanni na kasar Ukraine (2019-2020), shugaban kwamitin STB (2004-2018), Daraktan StarLightMedia (2012-2018), Shugaban Majalisar Ci Gaban Al'adu na Kasa, da gidan tarihi na Art and Museum Complex “Mystetsky Arsenal”.[3][4]

Tarihin Rayuwa[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Volodymyr Borodiansky a ranar 15 na watan Janairu 1974 a garin Novyi Rozdil, yankin Lviv. Mahaifinsa, Volodymyr Efimovych Borodiansky, ya yi aiki a matsayin mataimakin babban jagoran Novorozdilsk Production Association "Sera".[5]

Borodiansky ya kammala karatunsa a makarantar sakandare ta Novorozdolsk.[1]

Ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

A 1991, bayan kammala karatu daga makaranta, ya yi karatu a Sashin tattalin arziki na Lviv Agricultural Institute a Dublyany, Lviv yankin. Sannan ya koma Kyiv National Economic University a Faculty of Finance and Economics tare da digiri a kan kudi da kuma Credit. A 1997, ya sauke karatu daga Kyiv National Economic University.[6]

Mai sarrafa Media[gyara sashe | gyara masomin]

A shekara ta 2004, an zabe shi a matsayin ciyaman na hukumar STB.[7]

Daga 2012 zuwa karshen 2018 - ya zamo shugaban kungiyar watsa labarai ta StarlightMedia.[8]

A ranar 29ga watan Yulin 2019 Shugaba Zelensky ya nada Borodianskyi matsayin mai ba da shawara kan harkokin jin kai na kasashen waje.[9]

Volodymyr Borodiansky

A cikin shekara ta 2021, Borodianskyi ya zama memba na Hukumar Gudanarwa ta Media Group Ukraine. Ayyukansa sun haɗa da haɓaka canje-canje waɗanda za su kawo cigaba wajen watsaon wasanni na nishaɗi na fasaha da shirye-shirye ga marasa ilimi kuma za su tabbatar da ingancin tattalin arzikinta.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. 1.0 1.1 Бородянський Володимир Володимирович". Government of Ukraine (in Ukrainian). Retrieved 7 September 2019.
  2. Format Show 2011 Speakers". Kyiv Media Week. Retrieved 7 September 2019.
  3. “Lebed, Natalia (30 August 2019). "New faces of Ukrainian Cabinet: Who is who in government under PM Honcharuk?"
  4. https://www.president.gov.ua/documents/32020-31737
  5. Zelensky appointed STB channel chief as freelance advisor". Journalist.today. 29 July 2019. Retrieved 7 September 2019.
  6. Meet the Ministers: What We Know About Ukraine's New Cabinet". Hromadske International. 30 August 2019. Retrieved 7 September 2019.
  7. Рада затвердила склад нового Кабміну (список)". РБК-Украина (in Russian). Retrieved 13 May 2021.
  8. УКАЗ ПРЕЗИДЕНТА УКРАЇНИ №557/2019". Офіційне інтернет-представництво Президента України (in Ukrainian). Retrieved 13 May 2021.
  9. https://detector.media/infospace/article/186284/2021-03-24-volodymyr-borodyanskyy-stav-chlenom-naglyadovoi-rady-media-grupy-ukraina/