Walter Feghabo

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Walter Feghabo An haife shiba ranar 15 ga Agusta, 1956, a Warri, Jihar Delta. Najeriya. Ya tashi a Warri kuma ya halarci makarantun firamare da sakandare a cikin garin. [1]

Aiki[gyara sashe | gyara masomin]

Bayan ya kammala karatunsa na Sakandare, ya shiga aikin sojan ruwan Najeriya a shekarar 1976 a matsayin Kadet mai daraja, sannan kuma aka bashi mukamin Karamin-Laftanar a shekarar 1979. Walter Feghabo yakasance Kwamandan sojojin ruwa ne (mai ritaya) Walter Feghabo ya yi aiki a matsayin shugaban soja na farko a jihar Ebonyi[2] a Najeriya tsakanin Oktoba 1996 da Agusta 1998 bayan an kirkiro jihar Ebonyi daga wani sashi na jihar Enugu da kuma jihar Abia a lokacin mulkin soja na Janar Sani Abacha. Daga nan aka nada shi a matsayin mai kula da jihar Delta a watan Agustan 1998 a lokacin gwamnatin rikon kwarya ta Janar Abdulsalami Abubakar , inda ya mika wa zababben gwamnan farar hula James Ibori ranar 29 ga Mayu 1999.[3] 

Ritaya[gyara sashe | gyara masomin]

A watan Yuni 1999, duk tsoffin shugabannin soji na Abacha sukayi Ritaya daga gwamnatin tarayya, ciki har da Walter Feghabo

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. https://www.ebonyistate.gov.ng/governor.html
  2. https://ebonyistate.gov.ng/governor.aspx Archived 2023-07-19 at the Wayback Machine
  3. https://ebonyistate.gov.ng/governor.aspx Archived 2023-07-19 at the Wayback Machine