Wikipedia:Wikipedia Watan Asiya/2019

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Wikipedia Watan
Asiya 2019

Wikipedia Watan Asiya Gasa ce dake zuwa a duk watan Nuwamba ta kowace shekara, Wanda ke mayar da hankali akan daukaka abubuwan da suka kebanci Nahiyar Asiya a dukkanin harsunan Wikipedia daban daban. Kowace kungiya dake cikin gasar tana gudanar da edit-a-thon na tsawon wata daya, wato a Nuwamba, Anason a kirkiri sabbin (muƙaloli) bayanai a shafuka ko inganta shafukan da suka danganci nahiyar Asiya kawai, banda na daga kasashen ku, shiga gasar ba'a kebe kawai wa yan'Asiya ba, gasar kowa da kowa na iya shiga.

Wikipedia Watan Asiya

Ansoma gasar na farko ne a shekarar 2015, kuma duk shekara jimillan mukalar da ake samu karuwa sukeyi, suma masu shiga gasar sai kara yawa sukeyi. A shekaru uku da suka wuce ansami sama da 20,500 na ingantattun kasidu da aka sanya daga harsuna fiye da 50 na Wikipedia daga editoci sama da 2,000.

Kamar yadda aka saba, kawance da canjin al'ada na mutanen Asiya yasa duk wanda ke cikin gasar idan ya kirkiri sabbin shafuka hudu (4) to za'a bashi kyauta "special Wikipedia Postcard" daga wata kungiya dake a cikin gasar.

Kaimaza ka shirya dan za'a baka mamaki! bakasan wace kungiyar Wiki bace zata turo maka kyautar postcards! Editoci dasuka kirkiri ƙasidu masu yawa akowace Wikipedia za'a karramasu da girmamawan "Wikipedia Asian Ambassadors" wato sun zama jakadu na musamman na Watan Asiya.

Yi Rijista anan

Dokokin Gasa[gyara masomin]

A taƙaice: Anason a ƙirƙira sabbin Muƙala da ya danganci Asiya ne kawai, Misali kamar, mutane, wurare, al'adunsu, da sauransu (people, places, culture, etc.), akalla asamu 3,000 na bayits da kalmomi 300 ƙaranci, tareda madogararsu (shadar inda aka nazarto labarin(references)) a tsakanin watan Nuwamba ta 2019. Amma Banda ƙirƙiran jadawali (list or table).

 • Muƙalolin su zama sabbin ƙirƙira ne daga gareka, bawai ƙara yawan gajeren Muƙala akayi ba, daga 1 ga watan Nuwamba 2019 0:00 zuwa November 30, 2019 23:59 (UTC).
 • Muƙalan yazama yanada 3,000 na bayit da ƙarancin kalmomi 300. (exclude Infobox, template etc.)
 • Muƙalar yazama ya cimma ƙa'idar notability na Wikipedia.
 • Muƙalan suzama sunada Madogara (references) masu inganci, bayanai dabasu da tabbas ko sa'insa dole a sanya shaidar wadanda suka fadesu.
 • Muƙalolin kada suzama fassara zalla na komfuta amma kuma dole suzama ankofa sannan aka fassara ne.
 • Kada asamu matsaloli na hakkin masu ainihin mallaka, ko gaskiyar ingancin bayanan Muƙalar.
 • Banda ƙirƙiran Muƙala wadda jadawali ce kawai.
  • Saidai kawai: Idan aka ƙirƙira jadawalin da yazama Wikipedia Featured list a kirge.
 • Muƙalar yazama mai Isar da sako ne.
 • Muƙalar yazama yana bayani ne akan kowane irin abu ne daga ƙasashen nahiyar Asiya.
 • Muƙalolin da masu tsara gasar suka aika dole wasu masu tsara gasar ne zasu bincikesu.
 • Masu hukunci daga kowane harshe na Wikipedia zasu ƙayyade ko an yarda da Muƙala ko ba'a yarda da ita ba.
 • A sanda aka ƙirƙira Muƙala hudu da suka hada duk abinda ake nema, za'a turo maka da WAM postcard daga cikin Yankunan Wikipedia na Asiya.
 • Jakadu (Ambassadors) na Wikipedia Asiya zasu samu Satifiket dauke dasa hannu (signed certificate) daga Asian Affiliates, tareda karin postcard.

Yi Rijista[gyara masomin]

Zaku iya Rijista a kowane lokaci cikin watan Nuwamban nan.

Aika da Muƙaloli[gyara masomin]

Aika da Muƙalolin da kuka kirkira anan.

Idan ana samun matsala wurin tura aiki a nan, a shigar da bayanin matsalar anan.

Organizers[gyara masomin]