Wurin Tarihi na Bishiyar Agiya
Appearance
Wurin Tarihi na Bishiyar Agiya | |
---|---|
Wuri | |
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya |
Jihohin Najeriya | jahar Lagos |
Ƙananan hukumumin a Nijeriya | Badagry |
|
Wurin Tarihi na Bishiyar Agiya tana nan wurin da itacen Agia ta ke ( Egun: Asisoe Tin ) a kusa da babban ɗakin taro na Badagry.[1] Bishiyar ta Agiya ta kasance mai tsawon 160 feet (49 m) da fadin 30 feet (9.1 m).[2] Abin mamaki shine kasancewa a gindin bishiyar ne Thomas Birch Freeman da Henry Townsend suka fara wa'azin Kiristanci a Najeriya a ranar 24 ga watan Satumba, 1842,[3] [4] bishiyar ta rayu sama da shekaru 300 har sai da guguwa ta kayar da ita a ranar 20 ga watan Yunin 1959. [5]
A maimakon bishiyar, an gina wani dutse a shekarar 2012 don bikin cika shekaru 170 na Kiristanci a Najeriya.
Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Oluwadahunsi, Olawale (25 March 2015). "Badagry... -Footprints of slavery". National Mirror.
- ↑ History in Africa. African Studies Association. 1992.
- ↑ L. C. Dioka (2000). An Unsung Hero of the Church and Society: A Biography of Dominic Ogbonna Dioka L.C. Dioka.
- ↑ Ige, Betty (10 June 2014). "Badagry: Recapturing lost history". The Herald News. Retrieved 18 January 2016.[ permanent dead link ]
- ↑ Toyin Falola (1999). Yoruba Gurus: Indigenous Production of Knowledge in Africa. Africa World Press. pp. 220–. ISBN 978-0-86543-699-2