Ya'u Gwarmai

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Hon. Ya’u Gwarmai (an haifeshi ranar 3 ga watan Maris, 1970) a garin Gwarmai da ke cikin karamar hukumar Kunchi, a Jihar Kano. Ya kasance dan siyasa ne mai kishin al'ummar yan kinshi, dama kasa baki daya daya. An zabe shi a matsayin dan majalisar jiha sau biyu a shekarar 2015 da kuma 2019[1]

Karatu[gyara sashe | gyara masomin]

Hon. Gwarmai ya yi karatun framare kinsa a Danbatra Central a 1976, ya kammala kuma a 1982 da takardar shedan kamma framare. A1984 da 1987 ya cigaba da karatu kolejin ilimi mai nisa a kano (Continue Education Central, Kano) sannan daga bisani ya koma Jami'ar Bayero da ke Kano, Jihar Kano, daga 2012 zuwa 2014 don cigaba da karatun digiri na biyu (Masters) a fannin kasuwanci wato (MBA).

Siyasa[gyara sashe | gyara masomin]

Gwarmai ya fara siyasa a matsayin kansila bayan nan ya zama mataimakin sakatare sannan aka zabe shi a matsayin wakili (delegate) na jamiyyar su a matakin karamar hukuma sanna, ya zama wakili har ila yau a matakin jiha. Hon. Ya'u Gwarmai an zabe shi a matsayin dan majalisar jiha a shekarar 2011 zuwa 2015 da kuma 2015 zuwa 2019.[2][3]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]