Yahaya Dikko
Yahaya Dikko | |
---|---|
Rayuwa | |
Sana'a | |
Sana'a | injiniya |
Yahaya Dikko ya kasance mai kula da harkokin Nijeriya wanda ya kasance Janar Manaja na NEPA.[1] [2] sannan daga baya ya zama Mashawarci na Musamman kan Harkokin Man Fetur da Makamashi ga Shugaba Shehu Shagari . Ya kasance shugaban tawagar Nijeriya zuwa OPEC a lokacin gwamnatin Shagari sannan daga baya ya zama Shugaban OPEC. [3] Dikko ya kasance mai ba da shawara kan mai a shekara ta (1983) lokacin da farashin mai ya fadi a duniya kuma Najeriya da OPEC suka rage farashin mai, na farko tun lokacin da aka fara hana shigo da mai a shekara ta( 1973 ). [4]
Dikko an haife shi ne ga dangin Abdurahman Dikko. Ya yi karatu a Makarantar Midil ta Zariya da Kwalejin Kaduna. Ya halarci kwalejin fasaha ta Brighton. Dikko ya taba kasancewa Babban Sakatare na Hukumar Kula da Dam din Neja kuma Babban Manajan NEPA.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Schultz, Bonnie J., and Robert Rundblad. "African Update." Africa Report 23.2 (1978): 23. ProQuest. Web. 30 July 2018
- ↑ Schultz, Bonnie J., and Robert Rundblad. "African Update." Africa Report 23.2 (1978): 23. ProQuest. Web. 30 July 2018
- ↑ Atlas, Terry. "Once-Mighty OPEC Bickers to a Tenuous Accord." Chicago Tribune (1963-Current file), Mar 20 1983, p. 2. ProQuest
- ↑ PAUL LEWIS, Special to the New,York Times. "NIGERIAN OIL PRICE CUT SPURS URGENT TALKS WITHIN OPEC." New York Times, Late Edition (East Coast) ed., Feb 21 1983, ProQuest