Yakubu Yackson Sanda
Yakubu Yackson Sanda | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | 1965 (58/59 shekaru) |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan siyasa |
Yakubu Yakson Sanda (an haife shi a shekara ta 1965) ɗan, siyasar Najeriya ne daga Bicizà wanda aka zaɓe shi a matsayin kakakin majalisar dokokin jihar Filato ta tara a shekarar 2021.[1] Sanda shine ɗan, majalisa na farko da aka zaɓa daga Mazaɓar Pengana a jam'iyyar All Progressives Congress a shekara ta 2019. Ƴan majalisar ne suka zaɓe shi a matsayin, kakakin majalisar bayan tsige Rt. Hon. Abok Ayuba.[2][3]
Ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]Yakubu Yackson Sanda ya halarci kuma ya samu shaidar kammala karatunsa na farko a makarantar firamare ta UNA da ke acikin Jos, inda ya kammala karatunsa na Sakandare a Kwalejin Metropolitan, Jos.
Ya yi karatun Economics a Jami'ar Jos da ke Jihar Filato. Bayan haka, ya yi aiki da Hukumar Wasanni ta Jihar Filato a matsayin Akanta.
Sana'a
[gyara sashe | gyara masomin]A matsayinsa na ma’aikaci kuma Akanta daga Sana’a Yakubu Sanda ya samu muƙamin Daraktan kuɗi da samar da kayayyaki a ma’aikatan gwamnatin jihar Filato a ma’aikatar wasanni ta jihar Filato.
Ya taɓa yin aiki a Majalisar Wasanni ta Jihar Filato, da Akanta a Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Plateau HighLand, da Manajan Ƙungiyar ta Plateau United FC.
Siyasa
[gyara sashe | gyara masomin]Ya fara tafiyar sa ta siyasa tun yana matashi sama da shekaru 20 da suka wuce, lokacin da aka zaɓe shi ya jagoranci ƙungiyar ci gaban matasa ta Buji a matsayin shugaban ƙungiyar ta ƙasa.
Bayan haka ya tsaya takara a zaɓen majalisar dokokin jihar Filato a 2003, 2007, 2011 don wakiltar mazaɓar Pengana, wanda ya sha kaye.
A ƙarshe an zaɓe shi a matsayin ɗan majalisar tarayya a zaɓen 2019, kuma an zaɓe shi a matsayin shugaban majalisar bayan an tsige tsohon shugaban majalisar.
Rayuwa ta sirri
[gyara sashe | gyara masomin]Yakubu Yakson Sanda Kirista ne. Ya auri Nancy Yakubu Sanda kuma auren nasu da sukayi sun samu ƴaƴa uku.