Yellow Card (film)

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Yellow Card (film)
Asali
Lokacin bugawa 2000
Asalin harshe Turanci
Ƙasar asali Zimbabwe
Characteristics
Genre (en) Fassara thriller film (en) Fassara, comedy film (en) Fassara, drama film (en) Fassara da romance film (en) Fassara
During 90 Dakika
Direction and screenplay
Darekta John Riber (en) Fassara
External links

Yellow Card, fim ne na wasan kwaikwayo da soyayya na Zimbabwe da aka shirya shi a shekarar 2000 wanda John Riber ya ba da umarni kuma darakta da kansa ya shirya tare da matarsa Louise Riber.[1][2] Fim ɗin ya fito da Leroy Gopal a matsayin jagora yayin da Kasamba Mkumba, Collin Sibangani Dube, Dumiso Gumede, Ratidzo Mambo da kuma Kasamba Mkumba suka taka rawar gani.[3] Fim ɗin ya ta'allaka ne akan wani matashin ɗan wasan ƙwallon ƙafa wanda ya zama uban kyakkyawar yarinya bayan ya yi lalata da Juliet ba tare da kariya ba sannan kuma ya fuskanci sakamakonsa.[4][5]

An ɗauki fim din ne a birnin Harare na ƙasar Zimbabwe.[6] Fim ɗin ya fara fitowa a ranar 25 ga watan Disamba 2000.[7] Fim ɗin ya sami ra'ayi dabam-dabam daga masu suka.[8]

'Yan wasa[gyara sashe | gyara masomin]

  • Leroy Gopal a matsayin Tiyane Tsumba
  • Kasamba Mkumba a matsayin Juliet Bester
  • Lazarus Boora a matsayin Gringo
  • Collin Sibangani Dube a matsayin Skido
  • Dumiso Gumede a matsayin Coach
  • Ratidzo Mambo a matsayin Linda Karombo
  • Walter Muparutsa a matsayin Uban Tiyane
  • Pelagia Viaji a matsayin Mahaifiyar Tiyane
  • Yvette Ogiste-Muchenje a matsayin Rita
  • Pedzisai Sithole a matsayin Nocks

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "The World at His Feet". www.yellow-card.com. Retrieved 2021-10-09.
  2. "Yellow Card (2000)" (in Turanci). Retrieved 2021-10-09.
  3. "Filme aus Afrika: Film-Details". www.filme-aus-afrika.de. Archived from the original on 2021-10-09. Retrieved 2021-10-09.
  4. "Yellow Card : African Film Festival, Inc" (in Turanci). Retrieved 2021-10-09.
  5. "Yellow Card" (in Turanci). Retrieved 2021-10-09.
  6. "/ARTS & ENTERTAINMENT/CINEMA-ZIMBABWE: New Film To Be Seen By More Than 50m In Africa". Inter Press Service. 1999-11-30. Retrieved 2021-10-09.
  7. "YELLOW CARD by John Riber @ Brooklyn Film Festival" (in Turanci). Retrieved 2021-10-09.
  8. "Yellow Card" (in Turanci). Retrieved 2021-10-09.