Yusra Amjad
Yusra Amjad | |
---|---|
Haihuwa |
1992 Lahore |
Yusra Amjad mawakiyar Pakistan ce, marubuciya, kuma 'yar wasan barkwanci[1] wacce ke zaune a Lahore.[2]
Ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]Amjad ta kammala karatun digirin ta na farko a fannin Adabin Turanci (English literature) daga Jami'ar Forman Christian College da ke Lahore.[3] Yusrah kwararriyar masaniya ce kuma ta kammala MFA ɗinta a fannin rubuce-rubucen ƙirƙira daga kwalejin Sarah Lawrence, da ke New York a shekara ta 2022.
Rayuwa da Waƙa
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Yusrah Amjad a shekara ta Alif 1992 a Lahore, inda ta girma kuma a halin yanzu tana zaune a nan garin.[4] An buga waƙar Amjad a The Missing Slate, Crossed Genres, Cities+, The Rising Phoenix Review, and Where Are You Press. Wasan barkwancin ta na mata (feminist) [5] ya ƙunshi ra'ayoyin al'ummar Pakistan, mai dacewa ga desi woman.
Aiki
[gyara sashe | gyara masomin]Sha'awar Amjad ita ce ta wakilci muhimman batutuwa musamman da matan Pakistan ke fuskanta ta hanyar ban dariya. Waƙoƙinta suna nuna ɗabi'ar mata kuma suna da alaƙa akan karfafa mata. Itace wacce ta kafa kungiyar Auratnaak, wacce ke da nufin samar da wata al'umma ta mata waɗanda zasu iya ɗaukaka juna da wasan barkwanci, da kara karfafa gwiwar mata.
Wakilcin Zamantakewa
[gyara sashe | gyara masomin]Amjad ta gabatar da TEDx Talk a Lahore mai taken “On being young, unmarried, and female in Pakistan”. A matsayin ta na budurwar da ba ta yi aure ba, tayi tambaya kan matsalolin da matan aure ke fuskanta wajen kiyaye mutuncin su kuma cikin nadama ta ce al'ummar Pakistan ba ta son mata su zama manya a cikin al'umma. Ta karkare da cewa be kamata a hana gina al'umma bisa daidaiton jinsi, motsin mata, kwanciyar hankali na kuɗi, da matsayin zamantakewa ba.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "In the comedy of these Pakistani women, the joke's on misogynistic men". Arab News PK (in Turanci). 2019-03-08. Retrieved 2020-12-28.
- ↑ Lahore, Inside (2018-02-02). "The girl on fire". Inside Lahore (in Turanci). Retrieved 2020-12-28.[permanent dead link]
- ↑ "TEDxHabibUniversity | TED". www.ted.com. Retrieved 2020-12-28.
- ↑ "Yusra Amjad Archives". The Missing Slate (in Turanci). Retrieved 2021-10-26.
- ↑ Nasir, Amna (2016-09-12). "The Auratnaak Show: Pakistani Women Roast Patriarchy On Stage". Feminism In India (in Turanci). Retrieved 2020-12-28.