Jump to content

Zaɓen shugaban ƙasar Amurka a 2024

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Zaɓen shugaban ƙasar Amurka a 2024
United States presidential election (en) Fassara
Bayanai
Bangare na 2024 United States elections (en) Fassara
Ƙasa Tarayyar Amurka
Applies to jurisdiction (en) Fassara Tarayyar Amurka
Mabiyi 2020 United States presidential election (en) Fassara
Ta biyo baya 2028 United States presidential election (en) Fassara
Kwanan wata 5 Nuwamba, 2024
Gagarumin taron meeting (en) Fassara
Mai nasara Donald Trump
Ofishin da ake takara shugaban Tarayyar Amurka da Mataimakin Shugaban Ƙasar Taraiyar Amurka
Ɗan takarar da yayi nasara Donald Trump
Ƴan takara Donald Trump, Kamala Harris, Jill Stein (mul) Fassara, Robert F. Kennedy Jr. (mul) Fassara da Chase Oliver (en) Fassara
Tarihin maudu'i Timeline of the 2024 United States presidential election (en) Fassara
taswirar zaben amerika
american samoa. House election map

Zaɓen shugaban kasa na Amurka na 2024 zai zama zaben shugaban kasa na 60 na shekaru hudu, wanda za a gudanar a ranar Talata, 5 ga Nuwamba, 2024.[1] masu jefa ƙuri'a a kowace jiha da Gundumar Columbia za su zaɓi jerin masu jefa ƙuri'u zuwa babbar hukumar Zabe ta Amurka, wanda zai zaɓi shugaban kasa da mataimakin shugaban kasa na tsawon shekaru huɗu.

Shugaban kasar Joe Biden, memba na Jam'iyyar Democrat, da farko ya tsaya takara don sake darewa akan karagar mulkin kasar kuma ya zama dan takarar jam'iyyar a ranar 12 ga watan Maris a cikin wannan shekarar[2] Koyaya, biyo bayan abin da aka gani a ko'ina a matsayin kasawa ga shugaban kasar a cikin muhawara ta shugaban kasa wadda aka shirya a watan Yuni 2024 da ƙaruwar shekaru da damuwa game da rashin lafiya, wadannan dama wasu dsalilai irinsu sune suka saka shugaban kasar janyewa a matsayin dan takarar shugabancin kasar a ranar 21 ga Yuli. Kuma ya amince da Mataimakiyarsa Kamala Harris, a matsayin wadda zata maye gurbin sa takarar shugaban kasa a wannan rana. Ta samu cikakkiyar amincewar wakilai don zama sabuwar wadda aka zaba kwana daya daga baya a yar takarar shugaban kasar ta Amurka.[3][4] Ficewar Biden daga takarar ya sa ya zama shugaban kasa na farko tun lokacin da Lyndon B. Johnson a shekarar 1968 bai tsaya takara ba kuma Harris zata zama yar takara ta farko wadda bata shiga zaben fidda gwani ba tun lokacin da Hubert Humphrey ya kasance a wannan shekarar.

Wanda ya riga Biden, Donald Trump, mamba a Jam'iyyar Republican, yana neman sake zama shugaban kasar karo na biyu, wanda ba a jere ba, bayan ya sha kaye a hannun Biden a Zaben shugaban kasa na 2020. [5] Ya zama dan takarar jam'iyyar a ranar 12 ga watan Maris. A cikin takarar zuwa zaben, a ranar 30 ga watan Mayu, 2024, an yanke wa Trump hukunci kan laifuffuka 34 da suka shafi karya bayanan kasuwanci, ya zama shugaban Amurka na farko da aka same shi da laifi. A ranar 13 ga watan Yulin, an harbe shi a wani yunkurin kashe da akayi a wani taron kamfen a Pennsylvania.

Za a gudanar da zaben shugaban kasa a lokaci guda da Zaben Majalisar Dattijai ta Amurka, Majalisar, gwamna, da majalisar dokoki. An zabi Trump a lokacin Yarjejeniyar Jamhuriyar Republican ta 2024 a ranar 15 ga Yulin shekarar nan tare da abokin takararsa; Sanata Ohio J. D. Vance. Robert F. Kennedy Jr. ya fito ne a matsayin Dan takarar shugaban kasa na jam'iyya ta uku mafi girma tun lokacin da Ross Perot [6] a Zaben 1992, ya tsaya a matsayin mai zaman kansa. [7] [8] Ana sa ran manyan batutuwan kamfen su zama zubar da ciki, tsaron kan iyaka da shige da fice, Canjin yanayi, Dimokuradiyya, tattalin arziki, ilimi, Manufofin kasashen waje, kiwon lafiya.[9][10][11][12][13][14][15][16][17][18][19][20][21]

Wadanda suka lashe wannan zaben za'a rantsar dasu ne a ranar 20 ga Janairu, 2025, a matsayin shugaban kasa Na 47 da mataimakin shugaban Amurka Na 50, bi da bi.

  1. "Election Planning Calendar" (PDF). Essex-Virginia.org. Essex County, Virginia. Archived (PDF) from the original on February 7, 2016. Retrieved February 6, 2016.
  2. Kinery, Emma (April 25, 2023). "Biden launches 2024 reelection campaign, promising to fulfill economic policy vision". CNBC. Archived from the original on April 25, 2023. Retrieved April 25, 2023.
  3. Korte, Gregory; Fabian, Jordan (July 22, 2024). "Harris Has Enough Delegates to Clinch Nomination for President, AP Says". Bloomberg News. Retrieved July 22, 2024.
  4. Hutzler, Alexandra; Reinstein, Julia; Peller, Lauren; El-Bawab, Nadine; Sarnoff, Leah (July 22, 2024). "Election 2024 updates: Harris secures enough delegates to become presumptive nominee". ABC News. Retrieved July 22, 2024.
  5. Singman, Brooke (November 7, 2022). "Donald Trump announces 2024 re-election run for president". Fox News. Archived from the original on November 16, 2022. Retrieved November 16, 2022.
  6. Nuzzi, Olivia (November 22, 2023). "The Mind-Bending Politics of RFK Jr". Intelligencer. Archived from the original on March 6, 2024. Retrieved March 6, 2024. The general election is now projected to be a three-way race between Biden, Trump, and their mutual, Kennedy, with a cluster of less popular third-party candidates filling out the constellation.
  7. Benson, Samuel (November 2, 2023). "RFK Jr.'s big gamble". Deseret News. Archived from the original on November 21, 2023. Retrieved November 21, 2023. Early polls show Kennedy polling in the teens or low 20s
  8. Enten, Harry (November 11, 2023). "How RFK Jr. could change the outcome of the 2024 election". CNN. Archived from the original on November 20, 2023. Retrieved November 21, 2023.
  9. For sources on this, see:
  10. McCammon, Sarah (November 8, 2023). "Abortion rights win big in 2023 elections, again". NPR. Archived from the original on December 15, 2023. Retrieved December 16, 2023.
  11. "Here's why abortion will be such a big issue for the ballot come November". NBC. March 11, 2024. Archived from the original on March 11, 2024. Retrieved March 11, 2024.
  12. Sahil, Kapur (April 17, 2024). "7 big issues at stake in the 2024 election". NBC. Archived from the original on July 3, 2024. Retrieved April 17, 2024.
  13. Arnsdorf, Isaac. "Trump brags about efforts to stymie border talks: 'Please blame it on me'". The New York Times. Archived from the original on January 28, 2024. Retrieved January 29, 2024.
  14. Gongloff, Mark (January 30, 2024). "The 2024 election just might turn on ... climate change?". Portland Press Herald. Archived from the original on February 13, 2024. Retrieved February 12, 2024.
  15. Andreoni, Manuela (January 16, 2024). "Climate is on the Ballot Around the World". The New York Times. Archived from the original on January 16, 2024. Retrieved January 16, 2024.
  16. "Saving democracy is central to Biden's campaign messaging. Will it resonate with swing state voters?". CBS News. February 18, 2024. Archived from the original on March 13, 2024. Retrieved March 13, 2024.
  17. Cook, Charlie (March 2, 2023). "Will 2024 Be About the Economy, or the Candidates?". Cook Political Report. Archived from the original on March 25, 2023. Retrieved March 25, 2023.
  18. Manchester, Julia (January 29, 2023). "Republicans see education as winning issue in 2024". The Hill. Archived from the original on January 29, 2023. Retrieved July 9, 2023.
  19. Ward, Alexander; Berg, Matt (October 20, 2023). "2024: The foreign policy election?". Politico. Archived from the original on November 20, 2023. Retrieved November 20, 2023.
  20. Colvin, Jill; Miller, Zeke (November 27, 2023). "Trump says he will renew efforts to replace 'Obamacare' if he wins a second term". Associated Press News. Archived from the original on December 4, 2023. Retrieved December 4, 2023.
  21. "Here's where the 2024 presidential candidates stand on LGBTQ+ issues". ABC News. Archived from the original on December 6, 2023. Retrieved December 6, 2023.