Zakari Ziblim

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Zakari Ziblim
Member of the 1st Parliament of the 2nd Republic of Ghana (en) Fassara

1 Oktoba 1969 - 13 ga Janairu, 1972
District: Nanumba District (en) Fassara
Election: 1969 Ghanaian parliamentary election (en) Fassara
Rayuwa
Haihuwa 3 ga Afirilu, 1925 (98 shekaru)
Karatu
Makaranta Training College (en) Fassara certificate (en) Fassara : koyarwa
Sana'a
Sana'a Malami da ɗan siyasa
Imani
Addini Musulunci

Zakari Ziblim ɗan siyasan Ghana ne kuma memba na majalisar dokoki ta farko a jamhuriya ta biyu ta Ghana mai wakiltar mazaɓar Nanumba a yankin Arewacin Ghana a ƙarƙashin membobin jam’iyyar Progress Party (PP).[1]

Rayuwar farko da ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Zakari a ranar 3 ga Afrilun shekarar 1925 kuma ya zauna a Nanumba wani gari a tamale a Arewacin Ghana, Ya halarci Makarantar kwana ta Tamale da kuma Kwalejin Horar da Malamai ta Gwamnati . inda ya sami Takardar Horon Malamai daga baya kuma ya yi aiki a matsayin malami kafin ya shiga Majalisar.

Siyasa[gyara sashe | gyara masomin]

Ya fara siyasarsa a shekarar 1969 lokacin da ya zama ɗan takarar ɗan majalisa na wakiltar mazaɓar sa ta Nanumba a yankin Arewacin Ghana kafin a fara zaben majalisar dokokin kasar ta Ghana a shekarata 1969 .

An rantsar da shi a majalisar farko ta Jamhuriya ta Biyu ta Ghana a ranar 1 ga Oktoban shekarar 1969, bayan da aka ayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara a zaben kasar Ghana na shekarata 1969 da aka gudanar a ranar 26 ga watan Agusta 1969. Zamaninsa na dan majalisa ya kare ne a ranar 13 ga Janairun 1972.[2][3] [4]

Rayuwar mutum[gyara sashe | gyara masomin]

Ziblim musulmi ne.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Assembly, Ghana National (1970). Parliamentary Debates: Official Report (in Turanci). Ghana Publishing Corporation.
  2. The Legon Observer. Legon Society on National Affairs. 1969.
  3. Ghana Year Book (in Turanci). Daily Graphic. 1971.
  4. Chiefs and Politicians. Longman. 1979.