Jump to content

Zanen Ra'ayi, fitowar rana

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Zanen Ra'ayi, fitowar rana
Asali
Mahalicci Claude Monet
Shekarar ƙirƙira 1872
Asalin suna Impression, soleil levant da Impression, Sunrise
Movement Zanen Ra'ayi
haɗawa a Le Havre
Characteristics
Material (en) Fassara oil paint (en) Fassara da canvas (en) Fassara
Faɗi 63 centimetre (en) Fassara
Tsawo 48 centimetre (en) Fassara
Genre (en) Fassara marine art (en) Fassara
Description
Iconclass 46C223, 46C232, 24A1, 26B1, 46C21, 25H2322 da 22C5
Wuri
Place Musée Marmottan Monet (en) Fassara
Porto-Vecchio (mul) Fassara
Musée Marmottan Monet (en) Fassara
Tari Musée Marmottan Monet (en) Fassara
Inventory number (en) Fassara 4014
Mamallaki Musée Marmottan Monet (en) Fassara, Ernest Hoschedé (en) Fassara da Georges de Bellio (en) Fassara
Tarihi
Exhibitions 1st impressionist exhibition (en) Fassara
Notable events 1878
sales (en) — Faris
1985
art theft (en) Musée Marmottan Monet (en)
External links

Zanen Ra'ayi, fitowar rana wato Impression, Sunrise ( Faransanci : Impression, soleil levant ) wani zane ne wanda akayishi acikin shekara ta alif 1872 wanda Claude Monet ya fara nunawa wanda daga baya ya zamo sananne da "Baje kolin Zanukan Ra'ayi" a Paris a cikin watan Afrilun,acikin shekara ta 1874. An kuma ba da kyautar zanen tare da ƙarfafa sunan Kungiyar masu Zanen Ra'ayi.

Zanen Impression, Sunrise yana nuna tashar jirgin ruwa na Le Havre, garinsu Monet. Yanzu ana nuna su a Musée Marmottan Monet a Paris. [1]

Gidan mai daukar hoto Nadar, inda aka gudanar da nunin 1874
Ra'ayin zamani na tashar jiragen ruwa na Le Havre

Monet ya ziyarci garinsu wato Le Havre a arewa maso yammacin Faransa a cikin shekarar 1872 kuma ya ci gaba da ƙirƙirar jerin ayyuka da ke nuna tashar jirgin ruwa na Le Havre. Littattafan zanukan guda shida suna nuna tashar jirgin ruwa ne a lokaci daban daban "da asubahi, da rana, da maraice, da dare kuma daga ra'ayoyi daban-daban, wasu daga ruwan da kansa wasu kuma daga ɗakin otal suna kallon tashar jirgin ruwan".[2]

Zanen Impression, na Fitowar Rana ya zama mafi shahara a cikin jerin zanukansa bayan da aka fara gabatar dashi acikin watan Afrilun 1874 a Parisa a wani nuni da kungiyar "Masu Zane, Masu Sassaka, da dai sauransu. Inc." Daga cikin mahalarta talatin, Monet, Edgar Degas, Camille Pissarro, Pierre-Auguste Renoir, da Alfred Sisley ne suka jagoranci baje kolin, kuma sun nuna ayyuka sama da ɗari biyu waɗanda kusan mutane 4,000 suka gani, ciki har da wasu masu sukar rashin amincewa da salon.[3]

A cikin shekarar 1985 Philippe Jamin da Youssef Khimun ne suka sace zanen daga Musée Marmottan Monet . An dawo da shi kuma ya koma gidan kayan tarihi acikin shekarar 1990,[4] kuma an sake nuna shi a cikin shekara ta 1991.[5]

  1. Impression, Sunrise, Musée Marmottan Monet
  2. Brettell, Richard R. (2000). Impression : painting quickly in France 1860-1890. New Haven [u.a.]: Yale Univ. Press [u.a.] p. 126. ISBN 0300084463.
  3. Tomlinson, Janis, ed. (1995). Readings in nineteenth-century art. Upper Saddle River, N.J.: Prentice Hall. ISBN 0-13-104142-8.
  4. "The World's Greatest Art Heists". Forbes. 12 February 2008. Retrieved 16 November 2010.
  5. "Travel Advisory - Stolen Paintings Back in Paris Heists". The New York Times. 28 April 1991. Retrieved 16 November 2010.