Jump to content

Zanga-zangan 12 Yuni a Najeriya

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Zanga-zangan watan Yunin 12 a Nijeriya ta kasan ce zanga-zanga ce da za'ayi a watan yunin shekarar 2021 a Najeriya [1] wacce National Association of Nigeria Students (NANS) wato kungiyar dalibai na kasar Najeriya suka dabbaka,[2] saboda kara samun rashin tsaro da'a keyi a cikin kasar Najeriya, musamman ma ga dalibai a fadin Najeriya, wanda rashin tsaro ya samu da yawa daga cikin dalibai a fadin kasar, kamar wasu dalibai na greenfield da kuma sace dalibai a Jihar Neja, 12 watan yunin yayi daidai da bikin da za'a yi na murnan Dimokradiyya a Najeriya, saboda haka ne shugaban dalibai mai suna Sunday Asefon da shi da mambobin NANS suka dage cewa babu wani abin da ya dace a yi bikin Demokradiyya a Najeriya, saboda haka, sun ayyana wannan ranar mai zuwa a matsayin ranar zanga-zangar don yaki da rashin tsaro daya addabi dalibai a Najeriya.[3]

Tarihi[gyara sashe | gyara masomin]

Shugaban kungiyar dalibai na NANS mai suna Kwamared Sunday Asefon yana mamakin abin da yan kasar Najeriya zasu yi ma murna a ranar 12 ga watan Yuni na ranar dimokradiyyar Najeriya, lokacin da ake kashe dalibai da 'yan kasa tare da sace su a kowanne rana.

Asefon ya yi magana a kan wannan batun a wani taro da aka yi a jihar Ado-Ekiti, ya bayyana cewa rashin tsaro ya kai wani mataki na firgita, inda ba'a tabbatar da tsare ɗalibai ba koyaushe a makarantun dake fadin Najeriya.[3] inji shugaban kungiyar dalibai ta kasa (NANS).

A aani bangare na matakan kawo karshen barazanar a lokacin zanga-zangar, Asefon da mambobinsa sun kuma ayyana ranar 11 ga watan Yuni a matsayin ranar don gudanar da addu’o’i ga shuwagabanni da kuma jami’an tsaro, domin su yi nasara kan yan ta'adda, da kawo karshen kashe-kashe da satar mutane a duk fadin kasar.[3]

Duba kuma[gyara sashe | gyara masomin]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. editing (2021-06-01). "Nigerians Warm Up For June 12 Nationwide Mega Protests, Demand 14 Action Points". Sahara Reporters. Archived from the original on 2021-06-06. Retrieved 2021-06-06.
  2. "Insecurity: NANS declares June 12 day of protest". Punch Newspapers (in Turanci). 2021-06-01. Retrieved 2021-06-06.
  3. 3.0 3.1 3.2 "NANS declares June 12 national protest day as President seeks COAS' confirmation". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News (in Turanci). 2021-06-02. Retrieved 2021-06-06.