Jump to content

Ƙungiyan Bankuna na Access

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Ƙungiyan Bankuna na Access

Bayanai
Iri kamfani
Masana'anta financial services (en) Fassara
Aiki
Kayayyaki
Mulki
Hedkwata Victoria Island, Lagos
Mamallaki na
Tarihi
Ƙirƙira 1989
accessbankplc.com

Access Bank plc ko Bankin Access, cibiya ce ta hada hadan kudade da ajiyar su dake da helkwata a jihar Lagos Nijeriya. Bankin Access na da rassa daban-daban a fadin Afirka kuma kungiyar bankin Access ne ke da mallakin bankin. Kuma babban bankin Nijeriya ne ta basu ikon gudanarwa. Bankin na da abokan ciniki kimanin mutum miliyan 36.[1][2] Don mu'amala mai sauki ka danna *901#.

An kirkira bankin Access a shekara ta 1989. Adireshin helkwatar bankin na a rukunin dake 999c, Danmole Street off Adeola Odeku/Idejo Street, Victoria Island, jihar Lagos, Nijeriya amma daga baya ta koma zuwa Access Tower a Oniru Lagos.[3]

Jagororin Bankin Access

[gyara sashe | gyara masomin]

Babban jagoran kamfanin a Najeriya, na yanzu itace; Ms. Hadiza Ambursa. An nada ta matsayin Executive Director, Commercial Banking Division a watan Nuwamban shekara ta 2017. Mosun Belo-Olusoga; shi ne Babban mai umurni da gudanarwan na kamfani. Ayyukan da bankin access ke samarwa sun hada da bada bashi, Ajiya, Sa hannun jari, Ba yarda bashin gidaje, da sauran su. Adadin kudin shigan kamfanin US$298 million (NGN:59 billion) daga shekara ta (2015) Jimillar dukiyar kamfanin US$12.2+ billiyan (NGN:2.412 trilliyan) a shekara ta 2015.

Yawan ma'aikatan dake aiki a bankin Access sun kai sama da mutane dubu tara (9,000+) a shekara ta 2012

Headquarter wato Cibiyar kungiyoyin Bankin Access (na da) na nan a Plot 999c, Danmole Street, Off Adeola Odeku/Idejo Street, Victoria Island, Lagos, Nijeriya. A watan Febrairu shekara ta 2020, Cibiyar ta koma zuwa Access Tower, 14/15, Prince Alaba Oniru Road, Oniru, Lagos, Nigeria. Lambobin wuri na kasa wato coordinates of the banking groups headquarters are:06°26'00.0"N, 03°26'36.0"E (Latitude:6.433333; Longitude:3.443333).[4]


Siyan Bankin Diamond

[gyara sashe | gyara masomin]

A shekara ta 2018, Bankin Access ta yarda ta hade da Bankin Diamond wacce itama banki ce mai zaman kanta da ke fama da matsaloli na rashin jari mai karfi. Wanda siyayyar na bukatar yarjejeniya daga masu hannun jari daga duka bankunan.

  1. James Anyanzwa (3 November 2019). "Nigeria's biggest lender enters EA market to grow African footprint". The EastAfrican. Nairobi. Retrieved 31 August 2020.
  2. Faith Ikade (3 June 2020). "Access Bank Becomes Major Shareholder In Its Rwanda Subsidiary". Lagos: Ventures Africa. Retrieved 4 September 2021.
  3. Google (31 August 2020). "Location of headquarters of Access Bank Group"(Map). Google Maps. Google. Retrieved 4 September 2021.
  4. Google (31 August 2020). "Location of headquarters of Access Bank Group"(Map). Google Maps. Google. Retrieved 4 September 2021.