Ƙungiyar 'Yancin Dan Adam ta kasar Masar.
Kungiyar 'yancin Dan Adam ta kasar Masar المنظمة المصرية لحقوق الإنسان | |
---|---|
Bayanai | |
Iri | Kungiyar da ba ta riba ba |
Mulki | |
Hedkwata | Kairo |
Tarihi | |
Ƙirƙira | 1985 |
Wanda ya samar | |
en.eohr.org |
Kungiyar ''Yancin ɗan adam a Masar (EOHR), wacce aka kafa a watan Afrilu na shekara ta 1985 kuma tare da hedikwatar ta a Alkahira, Misira, kungiya ce mai zaman kanta kuma tana ɗaya daga cikin manyan hukumomi don kare' yancin dan adam a kasar ta Misira. [1] [2][3][4] Kungiyar tana bincike, saka idanu, da kuma bayar da rahoto game da take hakkin dan adam, kuma tana kare hakkin mutane ba tare da la'akari da ainihi, jinsi ko launi na wanda aka azabtar ba. An yi mata rajista da Majalisar Dinkin Duniya kuma tana aiki tare da wasu kungiyoyin kare hakkin dan adam.[5]
Matsayin EOHR na kasa da kasa.
[gyara sashe | gyara masomin]EOHR wani bangare ne na yunkurin kare hakkin dan adam na kasa da kasa da kuma na Larabawa. Tana aiki tare da hukumomin kare hakkin dan adam na Majalisar Dinkin Duniya, da kuma sauran kungiyoyin kare hakkin dan Adam na kasa da kasa da na yanki. An yi rajistar EOHR a Ma'aikatar Harkokin Jama'a a shekara ta dubu biyu da uku 2003 a karkashin rajista No. 5220/2003.
An bawa hukumar EOHR matsayi na musamman na ba da shawara tare da Majalisar Tattalin Arziki da Jama'a ta Majalisar Dinkin Duniya a shekara ta dubu biyu da shida 2006. Wannan matsayi na shawarwari yana bawa EOHR damar jin daɗin hulɗa da Majalisar Dinkin Duniya ta hanyar shiga cikin ayyukan Majalisar Dinkin ta Duniya, don 'Yancin Dan Adam, bisa ga shawarar ECOSOC 31/1996. Wannan yanke shawara an yi niyyar karfafa ka'idodin haƙƙin ɗan adam da aka tsara a cikin Universal Declaration of Human Rights, Vienna Declaration da duk sauran takardun haƙƙin ɗan Adam na duniya. Hukumar EOHR memba ce na kungiyoyi biyar na kasa da kasa wadda suka hada da: Ƙungiyar Larabawa don 'Yancin Dan Adam (AOHR), Ƙungiyar Duniya ta Kan Torture (OMCT), Ƙungiyar Ƙasashen Duniya don 'Yancin Dan adam (IFHR), Hukumar Shari'a ta Duniya (ICJ), da Ƙungiyar 'Yancin Magana ta Duniya (IFEX).
- ↑ "The Egyptian Organization for Human Rights". En.eohr.org. Archived from the original on 22 June 2018. Retrieved 28 September 2018.
- ↑ "Abuses escalate in Egypt". Archived from the original on November 17, 2015. Retrieved March 18, 2010.
- ↑ "Article: Egypt – Egyptian human rights defender faces years of imprisonment. | AccessMyLibrary – Promoting library advocacy". February 17, 2000. Retrieved March 18, 2010.
- ↑ "NewsLibrary.com – newspaper archive, clipping service – newspapers and other news sources". August 5, 2000. Retrieved March 18, 2010.
- ↑ "University of Minnesota Human Rights Library". 1.umn.edu. Retrieved 28 September 2018.