Jump to content

Abdu Gusau Polytechnic

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Abdu Gusau Polytechnic
Bayanai
Iri higher education institution (en) Fassara
Ƙasa Najeriya
Tarihi
Ƙirƙira 1992
sis.agpmafara.edu.ng
hoton Abdu Gusau da wasu

Abdu Gusau Polytechnic is a State government polytechnic located in Talata Mafara, Zamfara State, Nigeria.

An kuma kafa makarantar ne a shekara ta 1992, bayan tsohon gwamnan jihar Sokoto Yahaya Abdulkarim ya rattaba hannu a kan kudirin dokar kafa makarantar ‘Talata Mafara Polythecnic’. . Gwamnatin jihar Sokoto ta sauya sunan Polytechnic zuwa 'Abdu Gusau Polytechnic' a watan Fabrairun shekara ta, 1995. Anyi hakan ne domin karrama Marigayi Injiniya Abdu Gusau wanda ya rasu a watan Nuwamban shekarar 1994, bisa la'akari da irin gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban jihar. Jihar Zamfara ta Najeriya an kafa ta ne da wata doka ta Tarayya a shekarar 1996, kuma hakan ya sa aka mayar da polytechnic zuwa wani sabon wurin dindindin a Talata Mafara. Gwamnatin jihar Sokoto ba ta da alhaki a kanta, kuma ba bisa ka'ida ba a samu wata hukuma ta jihar Zamfara dake Sokoto..[1][2][3][4]

Polytechnic a yau, cibiya ce mai cikakken ci gaba tare da sassan 19, da ɗalibai guda 2524, [5] suna ba da shirye-shirye a fannonin karatu da yawa. Cibiyar a halin yanzu tana ba da ND's (National Diploma) a cikin darussa kamar; Mass Communication, Banking & Finance, Civil Law, Building Engineering, Electric Engineering and HND's (Higher National Diploma) a office management technology, business, bio chemistry, computer science and statistics.

  1. "HISTORY". agpmafara.edu.ng. 23 May 2020.
  2. "Historical Background of the Polytechnic". Abdu Gusau Polytechnic Talata Mafara. 23 May 2020. Retrieved 5 September 2020.
  3. NIPC (9 January 2019). "Nigerian States, Zamfara state". Nigerian Investment Promotion Commission. Nigerian Investment Promotion Commission. Retrieved 5 September 2020.
  4. Alapiki, Henry E. (2005). "State Creation in Nigeria: Failed Approaches to National Integration and Local Autonomy". African Studies Review. 48 (3): 49–65. doi:10.1353/arw.2006.0003. JSTOR 20065139. S2CID 146571948.
  5. https://agpmafara.edu.ng/