An haifi Abdul Baset ne a cikin iyalin Bedouin a Al-Bayadah, Homs . [1] kuma Kafin a juyin juya halin kasar Siriya, ya kasance mai tsaron ƙwallon ƙafa na Al-Karamah SC da Kungiyar kasar Siriya.[2] Lokacin da tashin hankali ya fara, ya jagoranci zanga-zangar a garinsu na Homs, inda ya dauki bakuncin 'yar wasan kwaikwayo Fadwa Soliman, tare da ita ya gudanar da tarurruka yana neman cire Shugaba Bashar al-Assad na kasar Siriya, da kuma sauran bukatun tashin hankali na Siriya. Yayin da tashin hankali ya ɓarke tsakanin kungiyoyi masu goyon baya da masu adawa da gwamnati, jami'an tsaro na kasar Siriya sun kashe dukkan 'yan uwansa hudu. An kashe kawunsa, Mohiey Edden al-Sarout, a watan Nuwamba na shekara ta alif dubu biyu da sha daya 2011 a Homs . [3] Ya zama sananne sosai saboda waƙoƙinsa a lokacin zanga-zangar adawa da gwamnati. Da farko, jawabinsa da waƙoƙinsa galibi na kasa ne a cikin yanayi, amma daidai da tasirin Islama tsakanin kungiyoyin 'yan tawaye na kasar Siriya, a hankali sun karɓi ƙarin addini da ƙabilu. A lokacin Siege na Homs daga shekara ta alif dubu biyu da sha daya 2011 zuwa shekara ta alif dubu da sha hudu 2014, ya zama kwamandan 'yan tawaye na Siriya. [4]