Abdul Rashid (mai noma)
Abdul Rashid (mai noma) | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | 4 ga Afirilu, 1950 (74 shekaru) |
ƙasa | Pakistan |
Mazauni | Islamabad |
Karatu | |
Makaranta |
University of Hawaiʻi (en) University of Hawaiʻi at Mānoa (en) |
Sana'a | |
Sana'a | biologist (en) |
Employers | Pakistan Academy of Sciences (en) |
Abdul Rashid, (an haife shi a shekara ta 1950) masanin kimiyyar noma ne a kasar Pakistan, wanda ya yi aiki a matsayin memba (Bio-sciences) na Hukumar Makamashi ta Atomic a kasar Pakistan (PAEC) daga shekara ta alif dubu biyu da a shirin da takwas 2008 zuwa shekara ta alif dubu biyu da sha daya 2011 kuma Darakta Janar na Cibiyar Binciken Aikin Gona ta kasar Pakistan (NARC) daga shekara ta alif dubu biyu da shidda 2006 zuwa shekara ta alif dubu biyu takwas 2008. Ya kammala karatun Ph.D. daga Jami'ar Hawaii a Manoa, Hawaii, a kasar Amurka.
Rayuwar ta farko da aiki
[gyara sashe | gyara masomin]Abdul Rashid ya yi nazarin hanyoyin karancin zinc a cikin shinkafa, alkama, da masara a shekara ta 1973 zuwa shekara ta 1979. Wadannan karatu da cibiyoyin sun kai shi ga matsayi na hadin gwiwa a Micronutrients Project a kasar Pakistan. Daga bisani ya koma yayai karatu a BSc (Honors) da MSc (Honurs) a Jami'ar Aikin Gona ta Faisalabad, a kasar Pakistan, kuma bayan ya sami tallafin karatu na Gabas da Yamma, ya sami PhD a fannin agronomy da kimiyyar ƙasa daga Jami'an Hawaii a Manoa, Honolulu, a shekara ta 1986. A can ya yi aiki a kan matsalar micronutrient, wanda ke da muhimmanci a gare shi da kasarsa a lokacin. Bayan kammala karatunsa, Abdul Rashid ya koma Cibiyar Nazarin Aikin Gona ta Kasa a Islamabad kuma ya fara nazarin amfanin ƙasa da abinci mai gina jiki.[1]
- ↑ "An Interview with 2017 IPNI Science Award Winner - Dr. Abdul Rashid" (PDF). Better Crops. International Plant Nutrition Institute. 2018.