Jump to content

Abdulrauf Lawan Saleh sarkin yakin arewa

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Abdulrauf Lawan Saleh[1] Dan kasuwane Kuma jajirtaccen Dan siyasa ya shahara wajen harkokin sadarwa da kuma safarar kayan abinci

Matashi ne wanda ya shahara wajen fafutukar neman na kansa ya kasance mutum mai kokarin kafa kasuwancin da alumma da dama zasu amfana. Shi ne mamallakin kamfanin ALSAM GENERAL MERCHANT wanda yake kasuwancin kayan abinci kamarsu waken suya, farin wake, shinkafa, masara dadai sauransu bayan haka yana da alakar [1]kasuwanci tsakanin shi da kamfanonin layukan sadarwa kamar Airtel, MTN, GLO, da 9mobile.

Matashin ya fara harkar siyasa a shekarar 2011, sannan a shekarar 2021, ne ya nuna bukatarsa ta fitowa takarar kansila a jam'iyyar PDP tsagin RABI'U MUSA KWANKWASO. Yanzu haka yana Jamiyyar ""New Nigeria People's Party"" NNPP

An haifashi a ranar 30 ga watan Nuwamban shekara ta alif dari tara da casa'in da shida 1996 a cikin birnin Kano dake Najeriya yankin afrika ta yamma.