Abor, Enugu

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Abor, Enugu

Wuri
Map
 6°28′30″N 7°24′30″E / 6.475°N 7.4083°E / 6.475; 7.4083

Abor gari ne, da ke kudu maso gabashin, Najeriya, a jihar Enugu kusa da birnin Enugu.

Garin Abor dai yana kan Titin Enugu- Nsukka, hanya mai matuƙar muhimmanci ga matafiya da ke zuwa arewacin Najeriya daga gabas. Ya ƙunshi ƙauyuka daban-daban guda takwas.

Ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

Abor gida ne ga Ikklesiya ta Cocin katolika guda biyu da manyan makarantu uku: Makarantar Sakandare ta Chist, Sakandaren Mata na St Theresa, da Makarantar Fasaha ta Girls.

Ƙauyuka[gyara sashe | gyara masomin]

'Ƙauyen Umuavulu: ɗaya daga cikin ƙauyuka takwas da suka haɗa da Abor, sananne ne ga mutane masu ƙwazo. Umuavulu Village yana da ƙauyuka 13: Umuozor, Eziagu, Nzuko, Umuoka, Uwenu na uwani, Umuikwo, Umuezike, Amaogwu, Ohemje, Aragu, Aguma, Orobo, da Ezionyia. Kowanne daidai yake da garinsa.shi

kadaiUbiekpo: Ya ƙunshi ƙauyuka shidda: Umuozor, Onuodagwu, Umudioku, Umuozi, Amaekwulu na Ebouwani, da Amagu.

Masana'antu[gyara sashe | gyara masomin]

Ƙauyen Umuezeani, ɗaya daga cikin ƙauyukan da ke yankin Abor, gida ne na Kamfanin Breweries na Najeriya 'Ama Greenfield Brewery, kamfani irinsa mafi girma a Najeriya.[1] Haka nan ma’adinan Onyeama na Kamfanin Coal na Najeriya yana nan kusa.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Waiting for the Brewing Pasture of Ama Greenfield". This Day Newspaper. 2004-11-16. Archived from the original on 2008-10-13. Retrieved 2008-04-12.

6°28′30″N 7°24′30″E / 6.47500°N 7.40833°E / 6.47500; 7.40833