Agbassa
Agbassa | ||||
---|---|---|---|---|
| ||||
Wuri | ||||
| ||||
Agbassa sunan ɗayan masarautun Urhobo guda biyu ne a Warri, jihar Delta, Najeriya, ɗayan kuma shine Okere-Urhobo.[1] Sunan 'Agbassa' asalinsa yazo daga Birtaniyya ne daga asalin sunansa AGBARHA, wanda har yanzu ake amfani da shi. Sarki na yanzu shine ; Mai Martaba Sarki, Orhifi, Ememoh II (JP) (Ovie Of Agbarha - Masarauta, Warri ) .[2]
Abinda ke ciki
[gyara sashe | gyara masomin]Akwai kusan al'ummomi bakwai waɗanda suka haɗu da masarautar Agbarha Warri (Agbassa):
- Otovwodo (Hedikwatar gargajiya)
- Igbudu
- Edjeba
- Ogunu
- Okurode (Okurode Urhobo)
- Oteghele
- Ukpokiti
A cikin Agbassa, ana yin bikin Iyerin kowace shekara, haka kuma ana yin bikin Esemor da Iniemor. Wani biki, wanda aka fi sani da Idju, ana kuma yin shi ne duk bayan shekaru biyu a duk cikin al'ummomin Agbassa, da Okere-Urhobo. Ana kiran wannan bikin da suna Agbassa Juju, kuma tana tsakiyar bautar Owurhie, wani allahntakar mutanen Warri.[2]