Agwaluma
Appearance
Agwaluma | |
---|---|
Conservation status | |
Near Threatened (en) (IUCN 3.1) | |
Scientific classification | |
Kingdom | Plantae |
Order | Ericales (en) |
Dangi | Sapotaceae (en) |
Genus | Gambeya (en) |
jinsi | Gambeya albida Aubrév. & Pellegr., 1961
|
Agwaluma wanda aka fi sani da farin tuffa, bishiya ce wadda take ƴaƴan a daji anfi samunta a duk faɗin Afirka. ana kiran wanann bishiyar da turanci da African star Apple haka ana yawan samun wannan bishiyar a Yammacin Afirka. Da yarbanci ana kiranta da Agbalumo da Yaren Igbo kuma udara.
Bishiyar agwaluma tana yin ƴaƴa a shekara sau ɗaya zalla ƴaƴanta sunfi nuna a lokacin hunturu, ƴaƴanta jajjaye ne haka cikin su kuma fari-fari ne. Hausawa sun aro kalmar Agwaluma ne daga yaren Yarbanci wanda su, suke kiran bishiyar da kuma Agbalumo su kuma Hausawa suka kirashi da agwaluma tunda babu shi a ƙasar Hausa.[1]
Amfaninta
[gyara sashe | gyara masomin]Ana shan agwaluma yanada zaƙi wani kuma yanada tsami, musamman mata tunba masu ciki ba.
- Agwaluma na maganin zazzabin Malaria mai naci ko wanda bai jin magani. Binciken wanda aka wallafa a kundin BMC Complementary and Alternative Medicine ya bayyana cewa wannan magani ka iya zama sabuwar karbabbiyar hanyar magance zazzabin duba da rashin nasarar da ake samu da sauran nau’ikan magunguna.
- Agwaluma dai na dauke da sinadarin Vitamin C, wanda ke da matukar amfani a jikin dan adam.
- Agwaluma na da matukar amfani ga mai dauke da juna biyu. Shan agwaluma na tsayar da amai da jiri wanda juna biyu ke haifarwa.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Plants of the World Online". Science.kew.org. Retrieved 18 January 2024.