Ahmad Babba Kaita

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Ahmad Babba Kaita
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

ga Yuni, 2019 - Mayu 2023
District: Katsina North
Rayuwa
Cikakken suna Ahmad Babba Kaita
Haihuwa 1968 (55/56 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Harsuna Turanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa Congress for Progressive Change (en) Fassara

Ahmad Babba Kaita (An haifi Kaita ne a ranar 8 ga watan Satumba, shekarata 1968), kuma bahaushe ne.[1]

Karatu da Aiki[gyara sashe | gyara masomin]

Ya yi karatun firamari a Sada Primary School dake a Kankiya tsakanin 1974 zuwa 1980. Ya koyi karatun addini saga wurin mahaifinshi. Ya yi karatu a kwalejin Kufena Wusasa Zariya a jihar Kaduna tsakanin 1980 zuwa 1985. Ya yi karatun digiri na farko akan sociology a Bayero University dake Kano a 1992, bayan ya kammala sai yayin bautar kasa a jihar Fatakut a shekar 1994 zuwa 1995. Bayan ya kammala bautar kasa yayi aiki a Splendid International Limited, daya daga cikin kamfanonin mai da iskar a Najeriya, har na tsawon shekara 15 wanda ya kai matsayin manajin darakta. Ya kuma yi aiki a Everglades Agencies Limited kafin ya shiga siyasa [3 1]Ya kuma kasance mamba na Majalisar wakilan Najeriya, wanda ke wakiltar kwantuwansin Kankia/Ingawa/Kusada Jihar Katsina, Najeriya. Ya zama mamba ne a shekarar 2011.[2]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. https://blerf.org/index.php/biography/babba-ahmad-kaita/
  2. "National Assembly | Federal Republic of Nigeria". Nassnig.org. Retrieved 2020-01-08.
  1. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-03-09. Retrieved 2023-03-09.