Akbar Hossain

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Akbar Hossain
Member of the Parliament of Bangladesh (en) Fassara


member of the 8th Jatiya Sangsad (en) Fassara

Rayuwa
Haihuwa Cumilla (en) Fassara, 18 ga Janairu, 1941
ƙasa Bangladash
British Raj (en) Fassara
Pakistan
Harshen uwa Bangla (en) Fassara
Mutuwa 25 ga Yuni, 2006
Yanayin mutuwa Sababi na ainihi (Ciwon zuciya)
Karatu
Makaranta University of Dhaka (en) Fassara
Harsuna Bangla (en) Fassara
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Kyaututtuka
Imani
Jam'iyar siyasa Bangladesh Nationalist Party (en) Fassara

Bir Protik Akbar Hossain (18 Janairu 1941 - 25 Yuni 2006) ɗan siyasan Bangladesh ne na Jam'iyyar Ƙasar ta Bangladesh. Ya taɓa zama ministan sufurin jiragen ruwa,ministan muhalli da gandun daji da kuma ministan man fetur da ma'adinai.

Tarihin Rayuwa[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Hossain a Kashari Patty a ranar 18 ga Janairu 1941, a gundumar Comilla.

Aikin soja[gyara sashe | gyara masomin]

Hossain ya shiga aikin soja a Kakul Military Academy a Pakistan a watan Mayun 1966, bayan kwamandan sa an tura shi zuwa 31 Baluch Regiment. Ya yin hidima, yayi karatun digirin sa na farko a Jami'ar Dhaka, in da ya sami digiri a 1969.

Hossain ya shiga yaƙin 'yancin kai a shekarar 1971 da farko ƙarƙashin Khaled Musharraf sannan kuma tare da rundunar Z ƙarƙashin jagorancin Ziaur Rahman. Anyi masa ado don wasan galantry, inda ya karɓi 'Bir Protik' saboda rawar da ya taka a Yaƙin. Bayan samun 'yancin kai, yayi ritaya na son rai daga sojojin Bangladesh a ƙarshen Disamba 1973, bayan ya samu muƙamin Laftanar Kanal.

Sana'ar siyasa[gyara sashe | gyara masomin]

Daga nan Hossain ya shi ga siyasa sosai kuma ya taimaka wajen kafa jam'iyyar United People's Party (UPP) a watan Janairun 1974. Yaci gaba da zama mataimakin shugaban jam'iyyar UPP. Acikin 1977, UPP ta haɗu da Jam'iyyar Jatiyatabadi,Hossain ya fita ya koma Bangladesh National Party (BNP) kuma ya taka muhimmiyar rawa wajen kafa ta.Da farko an naɗa shi sakatare na musamman sannan ya riƙe muƙamin babban sakataren haɗin gwiwa kuma yana ɗaya daga cikin mataimakan shugaban jam’iyyar BNP har zuwa rasuwarsa.

A cikin 1978, an nada Hossain a matsayin ministan albarkatun man fetur da ma'adinai a karkashin gwamnatin shugaba Ziaur Rahman. An fara zaben Hossain a matsayin dan majalisar dokokin Bangladesh a shekarar 1979, ya wakilci mazabar Comilla ta 8 a zaben Jatiyo Sangshad na 2, inda aka sake zabe shi har sau hudu. A lokacin mulkin kama-karya na soja na Janar Hossain Mohammad Ershad, an daure Akbar Hossain a lokuta daban-daban har sau biyar saboda ya shiga rikici da gwamnatin. [1] Bayan kawo karshen mulkin kama-karya na soji da kuma zaben Khaleda Zia, mace ta farko da ta zama Firaminista a kasar. Hossain ya koma gwamnati a matsayin Ministan Muhalli da dazuzzuka a watan Oktoba 1993.

A watan Oktoba na shekarar 2001, an nada Hossain a matsayin ministan sufurin jiragen ruwa bayan da jam'iyyar BNP ta jagoranci kawancen jam'iyyu hudu ta lashe zaben Jatiyo Sangshad na 8, da kashi biyu bisa uku, kuma Khaleda Zia ta zama Firaministan Bangladesh a karo na uku. Ya mutu a Dhaka a shekara ta 2006 sakamakon bugun zuciya mai yawa.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named sketch