Akintunde Sawyerr
Akintunde Sawyerr | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | 1964 (60 shekaru) |
Sana'a | |
Sana'a | Mai wanzar da zaman lafiya |
Akintunde Oluwole Sawyerr (an haife shi 6 ga Oktoba 1964) ɗan diflomasiyar Najeriya ne kuma ƙwararre a fannin dabaru, kiwon lafiya, da haɓɓaka aikin gona. A halin yanzu shine babban manajan darakta na farko na Asusun Lamuni na Ilimi na Najeriya (NELFUND), wanda aka naɗa a watan Afrilun 2024. [1] [2] [3] [4] [5] [6]
Rayuwar farko da ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Akintunde Sawyerr ranar 6 ga Oktoba 1964 a Landan. Ya fara karatunsa a Kwalejin Igbobi da ke Legas, Najeriya sai kuma Makarantar Royal Russell da ke Burtaniya. Daga nan sai ya yi karatu mai zurfi a Jami'ar Landan inda ya sami digirin farko BSc a fannin Chemistry. [7]
Sana'a
[gyara sashe | gyara masomin]Sawyerr ya riƙe mukamai da yawa a tsawon aikin da yayi. Daga 2013 zuwa 2018, ya yi aiki a matsayin shugaban yankin kudu da hamadar Sahara a Medtronic, mai kula da ayyukan yankin. Kafin wannan, a shekarar 2010, ya kasance mai bayar da shawara na ƙasa da ƙasa ga Rukunin Sarka da Kayayyaki a Hadaddiyar Daular Larabawa, yana bayar da shawara. [8] [9]
A 2009, Sawyerr shine a matsayin Darakta na Yankin Saharar Afirka a EBRAM Investments a Saudi Arabia. Har ila yau, ya ƙara samun ƙwarewa daga a fannin (life sciences, consumer products, and oil & gas sectors), inda ya gudanar da ayyuka a cikin ƙasashe 21 a nahiyoyin Gabas ta Tsakiya, Arewacin Afirka, da Turkiyya ga kamfanin DHL a shekarar 2007. A wannan shekarar, shi ne Shugaban Sarkar Kaya na Landan a DHL EXEL Supply Chain. [10] [11]
Sawyerr ya kafa Ƙungiyar masu fitar da kayayyaki (Produce Export Development Association -(PEDA), wadda aka fi sani da AFGEAN. Kungiyar haɗin-gwiwar ta karfafawa manoma sama da 2000, inda ta mayar da hankali kan magance asarar da ka iya biyowa bayan girbi dama fannin kasuwanci. [12] [13] [14] [15]
Jawabansa da faɗa-aji
[gyara sashe | gyara masomin]- COLEACP in Nigeria 2022.[16]
- Medtronic & GE Healthcare RTA in the United States.
- DHL Aviation on Agricultural exports from Nigeria to Europe.[17]
- Europe-Africa Business Heads of Government Forum in Brussels.[18]
- European Development Days (EU) in 2013.[19]
Rayuwa ta sirri
[gyara sashe | gyara masomin]Akintunde Sawyerr shine babban jikan Sofolahan Josiah Sawyerr. [20]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "EUROSPEED IMPORT/EXPORT LIMITED filing history - Find and update company information - GOV.UK".
- ↑ "Akin Sawyerr – Greenhills Farm". 2023-10-02. Retrieved 2024-04-19.
- ↑ "How Nigeria can ensure food security during the COVID-19 lock-down". www.cnbcafrica.com. 2020-04-24. Retrieved 2024-04-19.
- ↑ Nda-Isaiah, Jonathan (2024-04-05). "JUST-IN: Tinubu Appoints Sawyerr As NELFUND MD/CEO, Others". Retrieved 2024-04-19.
- ↑ Usigbe, Leon (2024-04-05). "Tinubu names Sawyerr as MD/CEO Nigerian Education Loan Fund". Tribune Online (in Turanci). Retrieved 2024-04-21.
- ↑ Nigeria, News Agency of (2024-04-18). "Tinubu's Student Loan Scheme: 1.2 million youths in first batch of beneficiaries". Peoples Gazette Nigeria (in Turanci). Retrieved 2024-04-21.
- ↑ "Akintunde Oluwole SAWYERR personal appointments – Find and update company information – GOV.UK". find-and-update.company-information.service.gov.uk. Retrieved 2024-04-19.
- ↑ "Akin Sawyerr". TechEmerge. Retrieved 2024-04-19.
- ↑ "Sawyerr urges FG to see shortfalls in agric supply chain as opportunities | Prompt News" (in Turanci). 2020-09-23. Retrieved 2024-04-20.
- ↑ https://www.pressreader.com/nigeria/the-guardian-nigeria/20201012/281784221563469. Retrieved 2024-04-20 – via PressReader. Missing or empty
|title=
(help) - ↑ "Businessday 06 jun 2018 by BusinessDay – Issuu". issuu.com (in Turanci). 2018-06-06. Retrieved 2024-04-20.
- ↑ Oka, Cynthia Dewi (March 2022). "Poet, Formerly Known as Activist, Formerly Known as Child Of God". The Massachusetts Review. 63 (1): 101–102. doi:10.1353/mar.2022.0015. ISSN 2330-0485.
- ↑ Partners, N. M. (2023-05-31). "Fluna Partners with AFGEAN to Help Nigerian Farmers and Exporters Grow and Boost Exports". Nairametrics. Retrieved 2024-04-19.
- ↑ "AFGEAN Showcases Nigeria's Processed Farm Produce In Belgium | Independent Newspaper Nigeria". 2018-06-08. Retrieved 2024-04-19.
- ↑ "How Nigeria plans to end informal exports – CNBC Africa". www.cnbcafrica.com. Retrieved 2024-04-19.
- ↑ Okojie, Josephine (2022-09-27). "COLEACP to support Nigeria's export drive for fresh produce". Businessday NG. Retrieved 2024-04-19.
- ↑ Sesan (2018-05-31). "Nigerian farmers to showcase produce in Brussels". Punch Newspapers. Retrieved 2024-04-19.
- ↑ "A decent life for all" (PDF). europa.eu. Retrieved 20 April 2024.
- ↑ "GreeHills Brochure" (PDF). greenhillsfarmstead.com. July 2021. Retrieved 20 April 2024.
- ↑ "Family Tree and Origin Information of Pa George and Manny Sawyerr". Ancestry.com (in Turanci). Retrieved 2024-07-05.