Jump to content

Aleksandar Mitrović

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Aleksandar Mitrović
Rayuwa
Haihuwa Smederevo (en) Fassara, 16 Satumba 1994 (30 shekaru)
ƙasa Saudi Arebiya
Karatu
Harsuna Serbian (en) Fassara
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
  Serbia national under-19 football team (en) Fassara2011-2013135
FK Teleoptik (en) Fassara2011-2012257
FK Partizan (en) Fassara2012-20132813
R.S.C. Anderlecht (en) Fassara2013-20156936
  Serbia national under-21 football team (en) Fassara26 ga Maris, 2013-201486
  Serbia men's national football team (en) Fassara7 ga Yuni, 2013-8957
  Newcastle United F.C. (en) Fassara2015-30 ga Yuli, 20186514
Fulham F.C. (en) Fassara1 ga Faburairu, 2018-30 ga Yuni, 20181712
Fulham F.C. (en) Fassara30 ga Yuli, 2018-19 ga Augusta, 202317397
  Al Hilal SFC19 ga Augusta, 2023-unknown value2828
 
Muƙami ko ƙwarewa Ataka
Lamban wasa 9
Nauyi 83 kg
Tsayi 189 cm
aleksandarmitrovic.com
Mitrovic
mitrovic
Aleksandar Mitrović

Aleksandar Mitrović (An haifeshi ranar 16 ga watan Satumba, 1994) kwararren dan wasa ne dan kasar Sabiya kuma dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Al Hilal wadda ke buga kofin Saudi Pro League kuma mai wakiltar kasar Sabiya.

Mitrovic

Yanasarar lashe gasar ta Serbian Superliga a shekarar shi ta farko a kungiyar .

Yana dan shekara 18, dan wasan yana daya daga cikin jerin yan wasa guda goma masu basira a lokacin na kasa da shekaru 19(U19) a yankin Turai wanda masu bada labarai na UEFA suka sanar.[3] Sannan sai ya koma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Anderlecht akan jumillar kudi £5m. Wannan cinikin nashi ya kasance babbar siyayya na tarihin kungiyar. Dan wasan ya buga wasanni har guda 90 a sabuwar kungiyar tashi inda ya samu damar zura kwallaye guda 44 a dukkanin gasar da ya buga a cikin shekaru biyu da yayi a ƙungiyar. Dan wasan ya samu nasarar lashe gasar Belgium Pro League a shekarar shi ta farko. A shekarar shi ta biyu kuma ya lashe kyautar gwarzon dan wasan da yafi kowa zura kwallo a raga a shekarar. A shekarar alif 2015 ya koma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Newcastle United akan jumillar kudi £13 miliyan. A shekarar alif 2018, yaje zaman aro a kungiyar kwallon kafa ta Fulham. Daga baya kuma ya koma dindindin inda ya taimaka ma kungiyar har suka samu nasarar tsallakawa buga babbar gasa ta Premier League.

A fannin kasa kuma, Mitrovic ya taimaka ma kasar Sabiya ta samu nasarar lashe European Championship U19 wanda aka buga a shekarar alif 2013. Kuma an zabi dan wasan a matsayin wanda yafi kowa a cikin gasar. Kuma a wannan shekarar ya fara buga wasa a matsayin kwararren dan wasa a kasar Sabiya. Dan wasan ya buga wasanni 90 a kasar tashi.

Dan wasan ya wakilci kasar tashi ta Sabiya a gasar cin kofin duniya wanda aka buga a shekarar alif 2018 da kuma wanda aka buga a shekarar alif 2022. Sai kuma UEFA Euro na shekarar alif 2024. Dan wasan shine dan wasan da yafi kowa yawan tarin kwallaye a tarihin kungiyar inda ya zura kwallaye 58 hakanne ya bashi damar zama zakakuri da yafi Kowane dan wasa yawan cin kwallaye a kasar. [4]

Rayuwar Gida

[gyara sashe | gyara masomin]

Mitrovic yana da yara guda biyu da abokiyar zamansa wato Kristina Janjic.[152] Dan wasan ya dade yana goyon bayan kungiyar kwallon kafa ta Partizan da kuma kungiyar kwallon kafa ta Newcastle United.[37][153][154]

Partizan

Serbian SuperLiga: 2012–13[5]

Anderlecht

Belgian Pro League: 2013–14[5]

Belgian Super Cup: 2014[5]

Newcastle United

EFL Championship: 2016–17[165]

Fulham

EFL Championship: 2021–22;[166]

EFL Championship play-offs: 2018,[53] 2020[82]

Al-Hilal[5]

Saudi Pro League: 2023–24

King Cup: 2023–24

Saudi Super Cup: 2023

Serbia U19

UEFA European Under-19 Championship: 2013[5]

Individual

Serbian SuperLiga Team of the Season: 2012–13[167]

UEFA European Under-19 Championship Golden Player: 2013[168]

UEFA European Under-19 Championship Team of the Tournament: 2013[169]

Belgian Pro League top scorer: 2014–15[170]

EFL Championship Player of the Month: March 2018,[50] April 2018,[51] October 2019,[70] October 2021[94]

Serbian Footballer of the Year: 2018,[171] 2022, 2023

UEFA Nations League top scorer: 2018–19,[172] 2022–23[173]

Fulham Player of the Year: 2019–20,[83] 2021–22[174]

PFA Team of the Year: 2019–20 Championship,[175] 2021–22 Championship[176]

EFL Championship Golden Boot: 2019–20,[177] 2021–22[178]

PFA Fans' Player of the Year: 2021–22 Championship[179]

EFL Championship Team of the Season: 2021–22[180]

EFL Championship Player of the Season: 2021–22[181]

King Cup top scorer: 2023–24