Jump to content

Ali Baba

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Ali Baba
Rayuwa
Haihuwa 21 Satumba 1975 (48 shekaru)
Sana'a
Sana'a ɗan wasan kwaikwayo, jarumi da cali-cali

Ali Baba jarumi ne a masana'antar fim ta Hausa wato Kannywood, Yana taka rawa a fannin nishadantar wa.[1]

Masana'antar fim

[gyara sashe | gyara masomin]

Baba Ari wato Ali baba kafin shigar sa Kannywood ya bude shagon zane zane da Kuma fenti, Wanda abinda ya karanta kenan, baba Ari ya fara Sha'awar fim ne tun yana firamare inda yaga yadda malamansu ke shirya musu dirama akan harkan ilimi, Ari baba ya kasance amini ga jarumi Cinnaka margayi, da Kuma Muhammad Mansoor sani Sharada (Mlm faram).

Ya auri mata guda biyu, daga baya ya rabu da dayar, yanzun da daya yake tare Kuma ita kadai ce ta haihu dashi ta haifi yaro namiji.

Ali baba , cikakken sunan sa shine Aminu Ali baba(Baba Ari) Haifaffen kofar nasarawa ne a Kano, ya kasance daya daga cikin masu wasan barkwanci a masana'antar fim ta Hausa, jarumi ne da yake fitowa a matsayin tsoho ya fito a Shirin tsoho, mutane da dama sukan dauka shi tsohon gaske ne Basu San matashi bane, Babu kamar sa da yake iya taka rawa a matsayin tsoho ba a Kannywood, Ali baba Yana da shekaru arba,in da hudu a shekarar 2022, Haifaffen Jihar Kano inda wasu ke masa kallon Dan jihar katsina Wanda karatu ne yakai shi can, yayi karatun firamare a jihar Kano makaranta Mai suna Balli special primary school bayan ya gama ya shiga makarantar gwamnati ta jiniya inda yayi karatun jiniya sakandiri a makarantar, bayan ya gama ya shiga makarantar siniya sakandiri ta gwamnati ta girma a shekarar 1990, bayan ya gama ya samu shiga makarantar kwalejin ilimi ta katsina inda yasami matakin karatu NCE, a kwas din (fine and applied art) harkan zane .

  1. https://dailytrust.com/aminu-ali-baba-the-funniest-man-in-kannywood/