Jump to content

Ali Ceesay

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Ali Ceesay
Rayuwa
Haihuwa Banjul, 10 Oktoba 1992 (32 shekaru)
ƙasa Gambiya
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
MŠK Žilina (en) Fassara2011-2011110
MŠK Žilina (en) Fassara2011-201340
MFK Zemplín Michalovce (en) Fassara2011-2012201
FC ŠTK 1914 Šamorín (en) Fassara2012-201290
Skonto FC (en) Fassara2014-201420
 
Muƙami ko ƙwarewa Mai buga baya

Ali Ceesay (an haife shi ranar 10 ga watan Oktoba 1992) ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na ƙasar Gambiya, wanda yake buga wasanninsa na karahe a kungiyar Skonto Rīga a Gasar Latvia High League.

Aikin kulob

[gyara sashe | gyara masomin]

MŠK Žilina

[gyara sashe | gyara masomin]

Ali Ceesay ya fara buga wasan kwallon kafa ne da kulob ɗin Samger. Ceesay ya koma Žilina a cikin bazarar 2011. Babban yayansa Momodou shima dan wasan kwallon kafa ne. Ali ya fara buga wasansa na farko a Žilina da Košice a ranar 25 ga watan Mayun 2011.[1]

MFK Zemplín Michalovce

[gyara sashe | gyara masomin]

Ceesay ya koma kulob ɗin Zemplín Michalovce a cikin watan Yulin 2011 akan lamuni na shekara guda daga Žilina. Ya fara buga wa kulob din wasa da Tatran Liptovský Mikuláš a ranar 23 ga watan Agusta 2011 a gasar cin kofin Slovak ta 2011–12. [2]

FC ŠTK 1914 Šamorin

[gyara sashe | gyara masomin]

A lokacin gasar bazara na 2012 Ceesay ya bar Žilina kuma ya sake komawa ŠTK 1914 Šamorín a matsayin aro na shekara guda.

Skonto Riga

[gyara sashe | gyara masomin]

A cikin watan Maris 2014 kulob din Latvia Higher League Skonto Rīga ya sanar da sanya hannu kan Ali Ceesay na kakar wasa mai zuwa. [3] Ya zama dan wasan Gambia na farko da ya taba taka leda a gasar Latvia. Ya bar kulob din a tsakiyar kakar wasa, ya kasa samun gurbi acikin ‘yan wasa goma sha ɗaya na farko.

  1. MFK Košice - MŠK Žilina 1:0 (0:0) Archived 2013-12-11 at the Wayback Machine 25.05.2011, mskzilina.sk
  2. MFK Zemplín zvíťazil aj v Liptovskom Mikuláši 25.08.2011, mfkzemplin.sk
  3. Pagājušās sezonas līderis Mingazovs atgriezīsies "Skonto" 03.03.2014, sportacentrs.com

Hanyoyin haɗi na waje

[gyara sashe | gyara masomin]