Aliyu Obaje

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Aliyu Obaje
Rayuwa
Haihuwa 1920
ƙasa Najeriya
Mutuwa 16 ga Yuli, 2012
Karatu
Harsuna Turanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Mai Martaba Aliyu Ocheja Obaje (1920 - 16 ga Yulin shekarar 2012) shi ne Sarki na 26 na Attah Igala (babban mai mulki) na Masarautar Igala a Nijeriya. Obaje ya kwashe shekaru 56 yana sarauta wanda hakan yasa ya zama daya daga cikin masu dadewa a harkar sarauta a tarihin Najeriya

Rayuwa da sarauta[gyara sashe | gyara masomin]

An haife shi a shekarar 1920, Aliyu Obaje shi ne mafi ƙanƙancin mutum da aka nada a matsayin Attah Igala; ya hau kan kujera yana da shekara 36 a ranar 2 ga Nuwamban shekarata 1956 bayan rasuwar magabacinsa Ameh Oboni. Obaje ya yi mulki na shekaru 52 kafin ya mutu yana da shekara 102. Fadar Masarautar Attah (wurin zama na mulki a Masarautar Igala) tana cikin tsohuwar garin Idah.

Ya kasance daya daga cikin masarautu mafi dadewa a Najeriya. Ya ba da yawan jama'a na masarautun gargajiya na kabilar Igala, ciki har da lakabin Agenyi-Attah na masarautar Igala, wanda aka bai wa Cif Ogwu J. Onoja, SAN. Aliyu Obaje shi ne shugaban majalisar sarakunan gargajiya ta jihar Kogi. Ya rike lambar girmamawa ta kasa ta GCFR (Grand Commander of the Federal Republic).

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

http://newsdiaryonline.com/attah-of-igaladr-aliyu-obaje-is-dead/ https://web.archive.org/web/20071105195958/http://www.newswatchngr.com/editorial/allaccess/nigeria/11021130529.htm https://www.vanguardngr.com/2012/07/attah-of-igala-longest-reigning-monarch-dies-at-102/ https://www.channelstv.com/2012/07/16/attah-of-igala-dies-aged-102/ https://www.premiumtimesng.com/news/93511-attah_igala_aliyu_obaje_dies.html http://saharareporters.com/2012/07/16/attah-igala-dies-102