Alphonsus Obi Igbeke
Alphonsus Obi Igbeke | |||
---|---|---|---|
25 Mayu 2010 - 6 ga Yuni, 2011 ← Joy Emodi - Stella Oduah → District: Anambra North | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | 1962 (61/62 shekaru) | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Karatu | |||
Harsuna |
Turanci Pidgin na Najeriya | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa | ||
Imani | |||
Jam'iyar siyasa |
Peoples Democratic Party Alliance for Democracy (en) |
Alphonsus Obi Igbeke wanda aka fi sani da Ubanese (An haife shi a shekarar 1962) a Nsugbe, arewacin Onitsha a jihar Anambra. Ya yi karatu a ƙasar Najeriya da ƙasar Amurka, inda ya sami PhD a fannin Injiniyanci. Da ya dawo Najeriya ya shiga kasuwancin kwangila, kuma ya zama ɗan kasuwa mai nasara tare da kadarori a Onitsha da Legas.[1]
Siyasa
[gyara sashe | gyara masomin]An rantsar da Alphonsus Obi Igbeke (wanda aka haifa a shekarar 1962) a matsayin Sanata mai wakiltar mazabar Anambra ta Arewa a jihar Anambra, Najeriya a ranar 25 ga watan Mayun shekarata 2010 bayan an soke zaben Joy Emordi na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP). Ya kasance memba na Jam'iyyar All Nigeria Peoples Party (ANPP).
Igbeke ya kasance mai neman zama ɗan takarar jam'iyyar PDP na kujerar majalisar wakilai a zaɓen shekarar 2003, amma ya gaza gabatar da shi. Ya canza sheka zuwa Alliance for Democracy (AD) kuma yayi takara a wannan dandalin, amma ya sha kaye a hannun dan takarar PDP. Ana zargin Igbeke da amfani da alakar sa ta siyasa don shirya kwamitin sauraron kararrakin zabe ya amince cewa an cire sunan sa daga cikin fitattun 'yan takarar PDP kuma an ayyana shi a matsayin wanda aka zaba.
A zaɓen watan Afrilu na shekarar 2007 na kujerar sanatan Anambra ta Arewa, Igbeke yayi takara a dandalin ANPP. An bayyana dan takarar PDP Joy Emordi a matsayin wanda ya yi nasara, hukuncin da ya daukaka kara. A ƙarshe Igbeke ya hau kujerar naki a Majalisar Dattawa ya biyo bayan hukuncin da kotun daukaka kara ta Enugu ta yanke wanda ya bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben sanata na shekarar 2007. Majalisar Dattawa ta ki amincewa da rantsar da shi bisa hujjar cewa ana ci gaba da daukaka kara, amma daga ƙarshe ta amince da hukuncin kotun. Taron Jam’iyyun Siyasar Najeriya (CNPP) ya yi kakkausar suka ga shugabannin Majalisar Dattawa kan jinkirin.[2]