Ambaliyar Afirka ta 2007
Ambaliyar Afirka ta 2007 | ||||
---|---|---|---|---|
ambaliya | ||||
Bayanai | ||||
Kwanan wata | 14 Satumba 2007 | |||
Wuri | ||||
|
Ambaliyar Afrika ta 2007, Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce ta kasance ɗaya daga cikin ambaliyar ruwa mafi muni a tarihi . Ambaliyar ta fara ne da ruwan sama a ranar 14 ga watan Satumba, shekarar 2007 lokacin gida. Sama da ƙasashe 14 ne bala'in ya shafa a Nahiyar Afrika, mutane 250 ne aka ruwaito ambaliya ta kashe kuma miliyan 1.5 ta shafa. Majalisar Ɗinkin Duniya ta ba da gargaɗi game da cututtukan da ke haifar da ruwa da kamuwa da fara.
Bayanai daga majiyoyin Afirka
[gyara sashe | gyara masomin]Ghana
[gyara sashe | gyara masomin]400,000 ba su da matsuguni inda a ƙalla mutane 20 suka mutu sannan an kwashe amfanin gona da dabbobi.
Wasu kauyukan da garuruwan yanzu sun goge taswirar ghana
George Azi Amoo - kodinetan kula da bala'o'i na Ghana
Sudan
[gyara sashe | gyara masomin]An bayar da rahoto na mutuwar mutane 64.
Habasha
[gyara sashe | gyara masomin]An bayar da rahoton mutuwar mutane 17. A yankin Afar kogin Awash ya yi sanadiyar rushewar dam. Kimanin mutane 4,500 ne suka maƙale, ruwa ya kewaye su.
Uganda
[gyara sashe | gyara masomin]Mutane 150,000 ne suka rasa matsugunansu sannan 21 aka ruwaito cewa sun mutu. Makarantu 170 ne ke karkashin ruwa.
Rwanda
[gyara sashe | gyara masomin]An bayar da rahoton mutuwar mutane 18 sannan kuma gidaje 500 ambaliyar ruwa ta tafi da su.
Mali
[gyara sashe | gyara masomin]Gada 5 sun ruguje sannan kuma gidaje 250 sun lalace.
Burkina Faso
[gyara sashe | gyara masomin]An bayar da rahoton mutuwar mutane har 33.
Kenya
[gyara sashe | gyara masomin]An bayar da rahoton mutuwar mutane guda 12.
Togo
[gyara sashe | gyara masomin]An bayar da rahoton mutuwar mutane guda 20.
Duba kuma
[gyara sashe | gyara masomin]- 2009 Ambaliyar Afirka ta Yamma
- Ayyukan guguwa na duniya na 2007
- Karancin ruwa a Afirka