Ambrose Folorunsho Alli
Appearance
Ambrose Folorunsho Alli (haihuwa ranar 22 ga watan Satumba, shekarar 1929– mutuwa ranar 22 ga watan Satumba, shekarar 1989).Farfesan likitanci ne a Najeriya, kuma wanda ya yi aiki a matsayin Babban Gwamnan Jihar Bendel ta kasar Najeriya (yanzu jihohin Najeriya Wanda suka hada da jihar Edo da jihar Delta ) tsakanin shekarar 1979 zuwa 1983. Shi ne gwamnan farar hula na farko.