Jump to content

Andrea Bottner

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Andrea Bottner
Rayuwa
Haihuwa Milwaukee (en) Fassara, 1971 (52/53 shekaru)
ƙasa Tarayyar Amurka
Sana'a
Sana'a Lauya


Andrea G. Bottner (an haife ta a shekara ta 1971 a Milwaukee) lauya ce ta Amurika, diflomasiyya, ƴan siyasan Jam'iyyar Republican, Ta kasance mai bada shawara kan siyasa kuma gwana akan Al'amuran mata, musamman tashin hankali ga mata. Tayi aiki a matsayin Darakta na siyasa a Ofishin Harkokin Mata na Duniya a Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurika a cikin Gwamnatin George W. Bush daga shekara ta 2006 zuwa 2009.[1]

Bottner tana da digiri na BA a kimiyyar siyasa daga Jami'ar Delaware da JD daga Jami'ar Baltimore makarantar shari'a. An shigar da ita a cikin Massachusetts Bar a shekara ta 2000, kuma ta yi aiki a matsayin lauya da ke wakiltar mata da aka yi wa duka kafin ta zama Mataimakin Shugaban Ma'aikata ga Kwamitin Jamhuriyar Republican Co-Chairman Ann Wagner; Bottner nada alhakin tsarin kulle mata ta kasa a lokacin neman zaben shugaban kasa na George W. Bush a shekara ta 2004.

Tayi aiki a cikin Gwamnatin George W. Bush a matsayin Babbar Mataimakiyar Darakta a Ofishin kan Tashin hankali kan Mata na Ma'aikatar Shari'a ta Amurika, a matsayin Mataimakiyar Daraktan wannan ofishin a shekara ta 2006 kuma a ƙarshe a matsayin Darakta na Ofishin Harkokin Mata na Duniya na Ma'aikatan Harkokin Wajen Amurika.[2] A matsayinta na Darakta ta kafa lambar yabo ta Mata ta Duniya ta Sakataren Harkokin Wajen Amurika. Bayan barin Ma'aikatar Harkokin Waje, Bottner ta kafa tsarin, Kamfanin Gwagwarmaya.

  1. Andrea G. Bottner, United States Department of State
  2. Andrea G. Bottner Appointed Acting Director of OVW Archived 2018-11-17 at the Wayback Machine, November 10, 2006